Home Labarai ‘Yan bindiga sun kashe malamin addini da yin garkuwa da mutum 10...

‘Yan bindiga sun kashe malamin addini da yin garkuwa da mutum 10 a Sokoto

8
0


‘Yan bindiga sun kashe malamin addini bayan garkuwa da mutane 10 a harin da suka kai kauyen gidan Kare a karamar hukumar Tureta jihar Sakkwato.Mazauni garin ya shaida manema labarai maharan sun kawo harin ne da safen ranar Alhamis in da suka tare mutane da ke dawowa da garin Tureta domin can ne suke kwana su dawo garinsu da safe domin kaucewa harin ‘yan bindigar a cikin dare.Majiyar ta ce maharan sun bude wuta ga mutane in da suka kashe mutum guda suka yi garkuwa da wasu sama da 10.”Mutane sukan kwana a garin Tureta domin gujewar harin ‘yan bindiga da safe a dawo gari kowa ya je gidansa, a haka muke tsawon lokaci kafin a kawo mana harin da ba mu zata ba.”Mutane da aka yi garkuwa da su Malam Dan Manga, Shehu da Hassan da Hussaini, Badaru da wasu yara biyu diyan Malam Ayuba, Saratu da wasu mutum biyu. Malam Dan Abu ya samu rauni a harin.An yi jana’iza ga wadanda suka rasa ransu da yawan mutane ba a gansu ba sun bace tun baya kawo harin da aka yi.Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda DSP Ahmad Rufa’i ya ce zai binciki babban jami’insu dake Tureta domin samun bayani, har zuwa hada rahoton ba a ji daga wurinsa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here