Home Labarai An kashe mutane sama da dubu 10 a Arewa cikin shekara biyu...

An kashe mutane sama da dubu 10 a Arewa cikin shekara biyu na mulkin Tinubu—Amnesty

9
0

Ƙungiyar kare hakkin bil’adama Amnesty Tace An kashe mutane sama da dubu goma 10,217 A arewa cikin shekaru biyu na Gwamnatin Tinubu

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International Nigeria ta ce akalla mutane 10,217 ne aka kashe a hare-haren ’yan bindiga a cikin shekaru biyu na farkon gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Amnesty International ta ce an samu asarar rayukan ne a jihohin Benue, Katsina, Kebbi, Plateau, Sokoto da Zamfara, inda Jihar Benue ta fi yawan mace-mace da mutane 6,896, sai Jihar Plateau da aka kashe mutane 2,630.

Isa Sanusi, Daraktan Amnesty International Nigeria, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki ne da alkawarin inganta tsaro, amma maimakon lamarin ya inganta, hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai sun ƙara ta’azzara.

A cewar Amnesty, a cikin shekaru biyu na farkon gwamnatin Tinubu, an samu bullar wasu sabbin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, ciki har da Lakurawa a jihohin Sokoto da Kebbi, da kuma Mamuda a Jihar Kwara.

Haka kuma, daruruwan ƙauyuka sun kasance cikin hare-hare ko kuma an tilasta wa mazauna barin gidajensu a jihohin Benue, Borno, Katsina, Sokoto, Plateau da Zamfara.

A Jihar Zamfara, Amnesty ta ce an kori jama’a daga ƙauyuka 638, yayin da wasu ƙauyuka 725 ke ƙarƙashin ikon ’yan bindiga a ƙananan hukumomi 13.

A Benue kuwa, Amnesty ta ce dukkan ƙananan hukumomi 23 na jihar sun fuskanci hare-haren ’yan bindiga, inda aka kori mutane daga sama da ƙauyuka 200, lamarin da ya haifar da gudun hijirar cikin gida na kimanin mutane 450,000.

A Plateau, an kuma samu hare-hare da dama, inda kimanin mutane 65,000 suka rasa matsugunansu sakamakon hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

Amnesty ta ce hare-haren sun kuma haifar da barazanar samun matsalar jin kai mai tsanani, musamman saboda mafi yawan waɗanda abin ya shafa manoma ne da suka kasa komawa gonakinsu.

Wasu daga cikin mutanen da suka rasa matsugunansu a jihohin Plateau da Katsina sun shaida wa Amnesty cewa sun koma bara domin samun abin da za su ci da kuma gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.

A yankin Dangulbi na Jihar Zamfara kuwa, manoma na kallon amfanin gonarsu na dankali mai zaƙi yana lalacewa, saboda ’yan bindiga sun hana su kai amfanin gonar kasuwar da ke kusa.

Amnesty International ta ce hukumomin Najeriya suna da alhakin kare rayukan jama’a, tare da tabbatar da cewa waɗanda ake zargi da aikata waɗannan kisan gilla da sauran laifuka sun fuskanci shari’a.

Isa Sanusi ya yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa da na zahiri domin dakile kashe-kashe, garkuwa da mutane da sauran laifukan da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke aikatawa.

Ya ce gazawar hukumomi wajen hukunta waɗanda ake zargi da aikata laifukan na ƙara haifar da yanayin da ake ci gaba da samun hare-hare ba tare da an kawo ƙarshensu ba.

Amnesty International ta ce dole ne a kawo ƙarshen zubar da jinin jama’a a faɗin Najeriya, tare da tabbatar da tsaron rayuka da hakkokin ’yan ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here