Home Rahoto ‘Yan bindiga sanye da kakin Soja sun kashe mutum huɗu a...

‘Yan bindiga sanye da kakin Soja sun kashe mutum huɗu a Sakkwato

51
0

A ƙalla an kashe mutane huɗu wasu da dama sun samu rauni a lokacin da ‘yan bindiga sanye da kakin Soja suka kawo hari a ƙauyen unguwar Lalle ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato.

Harin ya faru ne a jiya Lahadi 8pm zuwa 2am  na dare in da suka sace dabbobi da kayan shaguna da abubuwan gida.

Mazauna garin sun ce maharan sun yi yadda suke so tsawon awa shidda duk da akwai jami’an tsaro a yankin.

Maharan sun saci kayan amfani na gida sun fasa shaguna sun ɗebi kaya sun tafi da dabbobi da ba a san yawansu ba.

‘Yan gari sun ce ‘yan ta’addan aƙalla za su kai 200 da suka shiga ƙauyen ta kowane lungu sun shammaci mutane ne ganinsu da tufafin jami’an tsaro.

“Mun zaci sojoji ne ganin suna sanye da kakin soja sai da suka zagaye ƙauyen sannan suka fara harbi ga duk wanda yake da niyar tserewa, suka shiga gidajenmu suka sace dabbobi da kayan shagunanmu,” a cewar majiyar.

Mutanen da suka kashe Bilyaminu Wakkala da Ɗanbaki Tulunawa sai wasu mutum biyu dake zaune kusa ga ƙauyen Kongurus.

Mutanen sun ce ‘yan bindigar sun tafi da kusan awa ɗaya ne sannan sojoji suka zo da motocin yaƙi biyu in da suka kori wasu ‘yan bindiga a wani ƙauye in da suka kashe manomi guda.

A lokacin da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda DSP Ahmad Rufa’i ya tabbatar da kashe manomi a yankin amma ya ce har yanzu ba a bashi bayanin harin a ƙauyen ba.

“Na samu labarin tabbas an kashe mutum ɗaya a yanki ranar Lahadi. Sai dai har yanzu ba a bamu bayani kan ɗaya hari da aka kai a ƙauyen ba,” a cewarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here