Home Labarai ‘Yan Arewa suna tsinewa Rarara bayan da ya yi waƙar Zambo ga...

‘Yan Arewa suna tsinewa Rarara bayan da ya yi waƙar Zambo ga Pantami

23
0

Mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara na shan suka da tsinuwa a kafafen sada zumunta bayan yi wa ɗan takarar Gwamnan Gombe a PDP Farfesa Isa Ali Pantami waƙar zambo.

An rawaito cewa, mutane da dama ne suka yi rubuce-rubucen martani gare shi a kafafen sada zumunta, haka ma da yawan mutane sun tsine masa kan abin da ya yi na rashin mutunta Pantami saboda bambancin jam’iyya.

Masu martanin sun soki kalmomin da Rarara ya yi amfani da su a waƙar, inda suka bayyana cewa sukar siyasa bai kamata ta koma cin mutunci ba.

Wasu sun buƙaci a kiyaye matsayin Pantami na malamin addini, yayin da wasu suka bayyana cewa shiga siyasa yana ba da damar suka amma ya kamata a yi ta cikin hujja da ladabi.

Wasu sun tsinewa Rarara domin siffanta Pantami da mai shaye-shaye wannan na cikin rashin ladabi na ƙarshe da aka yi saboda siyasa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan labari, Rarara bai mayar da martani kan sukar da waƙar ta jawo ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here