Home Uncategorized Kano: An gano makaranta mai ɗalibai 1, 200 amma malamai 8 ne...

Kano: An gano makaranta mai ɗalibai 1, 200 amma malamai 8 ne kacal ke koyarwa 

168
2

Makarantar Sakandaren gwamnati ta Rufa’i  Tudun Wada da ke karamar Hukumar Doguwa, wacce ita ce karamar makarantar sakandare daya tilo a yankin, na da ɗalibai 1,200 amma malamai 8 kacal ke koyarwa a makarantar.

A wani bincike da jaridar DAILY POST ta yi, makarantar na da malamai na dindindin guda uku kawai sai kuma malaman sa-kai guda biyar, wadanda ke fafutukar kula da yawan daliban.

Binciken ya gano cewa a halin yanzu, makarantar na da rukunin ajujuwa biyu kacal, yayin da na ukun ya lalace, ba zai amfanu ba.

Wakilin jaridar ya kuma ruwaito cewa, ’yan kasuwa sun ciyo harabar makarantar, inda har ake sayar da bulo a farfajiyar makarantar.

Wakilin DAILT POST, wanda ya ziyarci yankin a wani bangare na binciken yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aiwatar da shirin bada agajin gaggawa kan ilimi na jihar, ya lura da cewa ana gina sabon rukunin ajujuwa amma ginin ya tsaya ko bai yi nisa ba.

Shamsuddeen Haruna, wani malamin sa kai wanda ya kwashe shekaru takwas ya na hidima a makarantar, ya bayyana cewa himma da jajircewarsa ga al’ummarsa ne suka sa ya ci gaba da koyarwa duk da mawuyacin hali.

2 COMMENTS

  1. Hi,

    I run an account on X with 800K+ active followers, and wanted to reach out about managarciya.com specifically.

    I just opened a $3/mo subscriber tier, and I’m inviting site owners in before opening it up publicly. The launch bundle includes:

    – A monthly retweet — I’ll amplify your best post each month to my followers.
    – 2 guides (WordPress Optimization + YouTube Traffic) with full resell rights — rebrand, use as lead magnets, or sell and keep 100%.
    – A new guide each month, same rights, plus the full back-catalog on signup.

    If this interests you, reply to this email and I’ll send over the account + the link — I’m only reaching out to a small number of sites initially.

    Sarah

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here