Tsohon shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Fakai dake jihar Kebbi Honarabul Musa Rabi’u (Jarman Fakai) ya rasu.
Marigayi Honabul Musa mataimakin Sakatare ne a kungiyar masu baiwa Gwamnan Kebbi shawara ya rasu a ƙalla yana shekaru 45 a duniya.
Maƙwabcin margayin Abubakar Anache ne ya tabbatar da rasuwar ya ce margarin ya kasance mutum mai gaskiya mai kishin al’umma da jajircewa wajen hidimtawa jama’a.
“Rasuwarsa babban rashi ne ba ga karamar hukumar Fakai kaɗai ba har ma ga Masarautar Zuru da Jihar Kebbi baki ɗaya.”
“An tsara gudanar da Sallar Jana’izar Marigayin a juma’a, cikin garin Mahuta da misalin karfe shida na yamma (6:00pm) kamar yadda iyalansa suka sanar.”
“Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa ya jikansa ya haskaka kabarinsa.”
Ɗan majalisar tarayya a yankin Zuru Honabul Kabir Ibrahim Tukura ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi.
Ya kuma ba shi Aljannatul Firdaus. Allah ya ba iyalansa ‘yan uwansa, da daukacin al’ummar Fakai hakurin jure wannan babban rashi.
Daga 📸 Abbakar Aleeyu Anache
