Tsadar Rayuwa: Zanga-Zanga Ba Mafita Ba Ce---Sarkin Musulmi

Tsadar Rayuwa: Zanga-Zanga Ba Mafita Ba Ce---Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya yi kira ga mutanen Nijriya su guji yin zanga-zanga domin ba ita ba ce mafita ba a halin da ake ciki na tsadar rayuwa a Nijeriya.

Sarkin Musulmi a kalaman da ya gabatar a fadar gwamnatin jihar Sakkwato a satin nan  a wurin taron tattaunawa kan halin da ake ciki da gwamnatin jiha ta kira mutanen jiha.

Ya ce tattaunawa kan abin da suka shafe mu abu ne mai kyau domin duk in da mutane suke akwai albarka mu 'yan uwan juna ne 

"Ba abin da ya buwayi Allah, kamata a koma a rika addu'a don neman taimakon Allah, mu anan Sakkwwato damuwarmu duk da matsala ta shafi ko'ina a Nijeriya, mun hadu ne domin ganin yanda da za a shawo kan matsalar, gwamnati ta yi tunani mai kyau wasu ba haka suke ba suna fita suna yin zanga-zanga wannan ba shi ne mafita ba, a taru a gaywa juna gaskiya shi ne zai fi samar da nasara shugabanni su shawo kan matsalolin da ake ciki.

"Yakamata mu zauna da shugabannin kungiyoyi mu tattauna su ba mu shawara, bayan zaman za mu sanar da gwamnati abin da ake ganin yakamata ta aiwatar don su ne mafita, gwamnati tana aiki ne domin talaka ba wai talaka ne zai yi wa gwamnati aiki ba.

"Ya zama wajibi a hada kai don taimakawa gwamnati a shawo kan matsalar, musamman rashin tsaro wadda ita ce ta hana mu samu noma da abinci a garuruwanmu don haka a daura damara wajen addu'o'i don ganin Allah ya sauwaka mana matsaloli," a cewar Sarkin Musulmi

Ya ce shugabanni kuma a koyaushe muna kira a ji tsoron Allah domin shugabancin da ya ba mu abin tambaya ne, a sani kuma gwamnati ta damu da halin da ake ciki, da ikon Allah sauki zai samu a cigaba da hakuri da addu'a a rika cigaba da yi wa shugaba addu'a.