Home Labarai Ka da Sarakuna su marawa jam’iyar Siyasa baya—Sarkin Musulmi 

Ka da Sarakuna su marawa jam’iyar Siyasa baya—Sarkin Musulmi 

16
0

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi tawagar masu rike da sarautun gargajiya a fadarsa da ke Sakkwato.

Zaman ya zo a daidai lokacin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, inda Sarkin ya yi kira ga uwayen ƙasa da su kasance masu nuna kyakkyawar tarba ga ’yan siyasa a lokacin da za su fara kai ziyara zuwa gundumomi da ƙananan hukumominsu domin neman goyon bayan jama’a a zaɓen 2027.

Daga nan ne Sarkin ya yi kira gare su da su guji shiga cikin harkokin jam’iyyun siyasa kai tsaye, tare da ci gaba da kasancewa masu adalci da haɗa kan al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here