Home Rahoto Tinubu ya umarci EFCC ta janye umarnin kotu na rufen asusun gwamnatin...

Tinubu ya umarci EFCC ta janye umarnin kotu na rufen asusun gwamnatin jihar Osun

6
0

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) da ta gaggauta komawa kotu domin janye umarnin da ya dakatar da asusun bankunan Gwamnatin Jihar Osun.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Tinubu ya ce ya ji takaici matuƙa game da lokacin da EFCC ta ɗauki wannan mataki, duk da cewa ya amince cewa hukumar ta yi hakan ne bisa ikon da doka ta ba ta bayan samun umarnin kotu a ranar 5 ga Agusta, 2026.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa duk wani mataki da wata hukuma ta tarayya ta ɗauka kan kasance ana danganta shi da shi a matsayin shugaban ƙasa, ko da kuwa bai san da shi ba tun farko.

Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa ta ba hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran hukumomin tsaro cikakken ‘yancin gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa da ba tare da tsoma bakin siyasa ba, yana mai cewa bai saba shiga harkokin gudanarwarsu ba.

Sai dai ya ce lokacin da EFCC ta ɗauki matakin ya sa ya zama dole ya sa baki, kasancewar saura kwanaki kaɗan a gudanar da zaɓen gwamnan jihar Osun.

A cewarsa, bai kamata a ɗauki wani mataki da zai haifar da zargin cewa ana amfani da wata hukuma ta gwamnatin tarayya wajen yin tasiri kan zaɓen ba.

Saboda haka, Tinubu ya ce ya umarci EFCC da ta gaggauta komawa kotu domin janye umarnin dakatar da asusun gwamnatin Osun tare da dakatar da duk wani matakin da ta fara ɗauka kan lamarin.

Umarnin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar ɗar-dar siyasa a jihar Osun gabanin zaɓen gwamna da za a gudanar a ranar 15 ga Agusta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here