Jagoran jam’iyyar NDC kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, Mista Peter Obi, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da cikakkiyar girmamawa a wurinsa, yana mai cewa ba zai taɓa zagin shugaban ƙasar ba duk da bambancin ra’ayin siyasa da ke tsakaninsu.
Peter Obi ya ce siyasa ba ta kamata ta zama hanyar cin mutunci ko zage-zage ba, yana jaddada cewa ana iya samun saɓanin ra’ayi kan manufofi ba tare da an wulakanta juna ba.
Ya ƙara da cewa yana ci gaba da sukar wasu manufofin gwamnatin Tarayya ne bisa abin da yake ganin ya dace, amma hakan ba yana nufin zai zagi ko raina Shugaba Tinubu ba.
Obi ya yi kira ga ‘yan siyasa da magoya bayansu da su riƙa gudanar da siyasa cikin mutunci, girmama juna da kuma kauce wa kalaman batanci.






