Home Rahoto Gwamnatin Sokoto ta ware naira biliyan 1.59 domin sayen motocin Hilux 30...

Gwamnatin Sokoto ta ware naira biliyan 1.59 domin sayen motocin Hilux 30 ga jami’an tsaro

16
0

Gwamnatin jihar Sokoto ta amince da bayar da kwangilar sayen sababbin motocin sintiri ƙirar Toyota Hilux guda 30 a kan kuɗi naira biliyan 1 da miliyan 592 da dubu 250 domin ƙarfafa dakarun tsaro a yaƙin da suke yi da ‘yan bindiga.

Sanarwar da darakta janar na yaɗa labarai na Gwamnatin Abubakar Bawa, ya fitar ta bayyana cewa an amince da wannan mataki ne a ƙarshen taron majalisar zartarwa ta jihar karo na takwas wanda Gwamna Ahmed Aliyu ya jagoranta.

Wadannan motoci guda 30 na a matsayin ƙari a kan sama da motocin Hilux 200 da motoci masu sulke guda 62 da gwamnatin ta riga ta sayo tare da raba wa hukumomin tsaro domin yaƙar ayyukan ta’addanci da sauran laifuka a jihar.

Haka kuma, majalisar ta amince da ƙudirin dokar hana ayyukan ‘yan bindiga ta musamman ta Jihar Sokoto ta shekarar 2026, a wani ɓangare na matakan doka domin hukunta masu ɗauke da makamai da daƙile ayyukansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here