Home Rahoto Tinubu Ya Dakatar Da Wasu Manyan Sakatarori Uku Bayan Sake Gano Wata...

Tinubu Ya Dakatar Da Wasu Manyan Sakatarori Uku Bayan Sake Gano Wata Sabuwar Hukumar Bogi

14
0



‎Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin kama wani mutum mai suna George Buchi Nwabueze nan take, tare da dakatar da manyan sakatarorin dindindin uku bayan Hukumar ICPC ta gano wata sabuwar hukumar bogi da ke aiki a cikin Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF).

‎Mutanen da aka dakatar su ne M.S. Danjuma, Nadungu Gagare da Richard P. Pheelangwah, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.

‎Shugaban ICPC, Dr Musa Aliyu, SAN, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa ranar Juma’a, bayan ya sake yi wa Tinubu bayani kan binciken da hukumar ke gudanarwa.

‎Ya ce an gano wata cibiya mai suna “National Brands Development and Made-in-Nigeria Special Project Office”, wadda aka ware mata ofishi a harabar OSGF ba tare da izinin shugaban ƙasa ba, kuma hakan ya saba wa dokokin gwamnati.

‎A cewar Aliyu, binciken ya nuna cewa Prince George Buchi Nwabueze ne ke jagorantar wannan hukumar bogi, tare da wasu mutanen da ake zargin suna taimaka masa a cikin OSGF.

‎Ya kuma bayyana cewa Nwabueze na amfani da wasu sunaye daban-daban, ciki har da George Nathan, George Nathan Nwabueze, Honourable George Buchi Nwabueze, Prince George Buchi Nwabueze da George Nwabueze.

‎Shugaban ICPC ya ce hukumar za ta ci gaba da bincike domin gano cikakken bayani kan yadda aka kafa hukumar bogin da kuma mutanen da ke da hannu a cikinta.

‎Wannan sabon binciken ya biyo bayan gano wata “Presidential Foreign Intervention Promotion Council” ta bogi, wadda wani Adeniyi Adeyemi Matthew ke ikirarin jagoranta. A halin yanzu yana fuskantar shari’a kan zargin jabun takardu da yin kwaikwayon wani.

‎Rahoton wucin-gadi na ICPC da aka gabatar wa Tinubu a ranar 6 ga Agusta ya kuma bayyana wasu hukumomi biyu da ake zargin na bogi ne, wato FCT Investment Promotion Agency da Foreign Investment Promotion Agency and Public-Private Partnership.

‎Sabuwar hukumar da aka gano ita ce ta huɗu cikin hukumomin bogi da ICPC ta gano tun bayan fara binciken lamarin a watan Afrilu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here