Tambuwal Tare Da Gwamnoni Uku Suna Zawarcin  Wani Tsohon Gwamna Ya Dawo PDP

Tambuwal Tare Da Gwamnoni Uku Suna Zawarcin  Wani Tsohon Gwamna Ya Dawo PDP
Alamar PDP

Tambuwal Tare Da Gwamnoni Uku Suna Zawarcin  Wani Tsohon Gwamna Ya Dawo PDP
Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranci gwamnoni uku a jihar Ondo in da suka tattauna da tsohon gwamna Olusegun Mimiko.
Gwamnonin da suke tare da  Tambuwal su ne Seyi Makinde, Nyesom Wike da Okezie Ikpeazu na  Oyo, Rivers da  Abia.
An yi tattaunawar a sirrance tare da makusantan tsohon gwamna wadda aka danganta da lallaɓar Mimiko ya dawo PDP.

Wani mai sharhi kan lamurran siyasa na ganin ziyarar ƙarara tana da nasaba da yunƙurin gwamnonin na dawo da su jagorori cikin jam'iyar ta PDP.