Home Labarai Sokoto: Miyagun ƙwayoyi na ƙara ta’azzara matsalar tsaro—-Ahmad Aliyu 

Sokoto: Miyagun ƙwayoyi na ƙara ta’azzara matsalar tsaro—-Ahmad Aliyu 

9
0

 
Gwamnan Sakkwato Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto ya ƙara tabbatar da gwamnatinsa ta himmatu wajen kawar da tu’amali da miyagun ƙwayoyi da safarar su a cikin al’umma.Gwamna ya tabbatar da hakan ne a wani jawabi da ya gabatar Alhamis kan ranar faɗa da miyagun ƙwayoyi na 2026 wnnda majalisar ɗunkin duniya ta ware ake yi  kowace shekara da aka yi a ɗakin taro na makarantar hardar Ƙur’ani ta Sarkin Musulmi Macciɗo.Gwamna Ahmed ya bayyana tu’amalli da miyagun kwayoyi yana cikin ƙalubale mafi hatsari a cikin al’umma, da ke rushe dangi ya sa matashi ya koma baya da wani amfani, ga kuma taimakawa wurin aikata manyan laifuka bayan sanya ka cikin matsalar rashin lafiya da shiga cikin hatsari.Ya nuna damuwarsa yanda matsalar safarar miyagun ke girma ita ce ke ƙara sanya aika ta manyan laifuka da raina jami’an tsaro na cikin gida da waje.Gwamnan ya bayar da ƙarfi kan yaƙar shan miyagun kwayoyi ba zai tsaya ga jami’an tsaro kawai ba, akwai buƙatar a haɗa kai a yi aiki tare tsakanin uwaye da malaman boko da malaman addini da sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin sa kai, da ma’aikatan lafiya da jagororin al’umma da manema labarai don tabbatar da an kawar matsalar a cikin al’umma.Gwamna wanda mataimakin sa Idris Muhammad Gobir ya waƙilta ya tabbatar da gwamnatinsa za ta ba da goyon baya ga duk wani shiri da zai dakile shan miyagun kwayoyi, da safararsu.Gwamnan ya yabawa hukumar NDLEA kan yaki da shan miyagun kwayoyi da take yi, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da hada kai domin tseratar da matasa masu tasowa a kuma gina ingatacciyar lafiya a tsakanin al’umma.A jawabin maraba Kwamandan hukumar Mustafha Gidado ya bayyana shan miyagun kwayoyi ba kawai barazana ne ga harkar tsaro ba har da kiyon lafiyar jama’a.Ya godewa gwamnati kan goyon bayan da ake ba su, ya yi fatar lamarin zai dore.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here