Sojoji sun yi nasarar kuɓutar da mutane shidda da aka yi garkuwa da su a Kebbi
Sojoji ƙarƙashin rundunar fansar yamma sun kuɓutar da mutane shidda da aka yi garkuwa da su a Kebbi bayan bayanan sirri da suka samu kan harin ‘yan ta’adda a ƙauyen Mehinua dake kan hanyar Bagudo a Kebbi.






