Home Siyasa Shugaban ƙasa ya ƙara yawan jihohin da zai je kamfe

Shugaban ƙasa ya ƙara yawan jihohin da zai je kamfe

31
0

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ƙara yawan jihohin da zai je kamfen ɗinsa daga 12 zuwa 19, baya ga Abuja, inda ake sa ran zai halarci tarukan yaƙin neman zaɓe guda 20 cikin 37 da jam’iyyar APC ta shirya a faɗin ƙasar.

Sabbin jihohin da aka ƙara sun haɗa da Katsina, Taraba, Zamfara, Imo da Kwara, yayin da aka kuma saka Akwa Ibom, Jigawa da Kebbi bayan ziyarar kamfen da ya kai jihohin a baya-bayan nan.

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa wasu daga cikin dalilan sauya jadawalin sun haɗa da buƙatar gwamnonin APC na Tinubu ya ƙaddamar da ayyukan raya ƙasa, da kuma ƙalubalantar ƙoƙarin ’yan adawa na nuna cewa shugaban ƙasar ba zai iya gudanar da kamfen a faɗin ƙasar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here