Kasar Saudiyya Ta Ki Ƙara Wa Najeriya Adadin Mahajjatan 2027
Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta ce Saudiyya ta ƙi amincewa da buƙatar Najeriya na ƙara yawan kujerun aikin Hajjin 2027, inda ta bar Najeriya da adadin mahajjata 50,000.
NAHCON ta ce ta tattauna da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya domin neman ƙarin kujeru, saboda karuwar masu son zuwa Hajji. Sai dai Saudiyya ta ce ƙarancin wurare da kuma ƙa’idojin rabon adadin mahajjata tsakanin ƙasashe ne suka sa ta ƙi amincewa da buƙatar.
Daga cikin kujerun 50,000, mahajjata 35,000 za su kasance ƙarƙashin gwamnati, yayin da 15,000 za a ware wa kamfanonin shirya aikin Hajji masu lasisi.
Shugaban NAHCON, Ambasada Ismail Yusuf,ya ce wa’adin shigar da bayanan mahajjatan 2027 a dandalin Nusuk shi ne 26 ga Satumba 2026, kuma ba za a ƙara wa’adin ba. Ya shawarci wadanda ba su samu kujerar 2027 ba kada su yanke ƙauna, domin tuni aka fara rajistar aikin Hajjin 2028.





