Home Rahoto Sarkin Musulmi ya baiwa Murtala Ɗan’iya sarautar Dallatun Sokoto

Sarkin Musulmi ya baiwa Murtala Ɗan’iya sarautar Dallatun Sokoto

11
0

Fitaccen ɗan kasuwa ya samu  sarautar Dallatun Sakkwato daga Sarkin Musulmi 

Daga Nasiru Bello Sakkwato 

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya amince da naɗin fitaccen ɗan kasuwa kuma mai ayyukan jin ƙan al’umma ɗan asalin jihar Sakkwato Alhaji Murtala Abdulkadir Dan’iya, a matsayin Dallatun Sakkwato.

Sarautar Dallatun Sakkwato tana cikin sarautu masu muhimmanci a jihar, sama da shekaru huɗu bayan rasuwar wanda ke riƙe da sarautar ba a baiwa kowa ba sai yanzu.

Wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 22 ga Yuli, wadda Sakataren Majalisar Masarautar Sakkwato kuma Danburam Sakkwato, Alhaji Sa’idu Muhammadu Maccido ya sanya wa hannu, ta ce an ba shi sarautar ne saboda girmamawar da yake nunawa Masarautar Daular Usmaniyya da kuma gudummawar da yake bayarwa wajen bunƙasa addinin Musulunci da cigaban al’umma.

Wasiƙar ta kuma yaba da ayyukan jin ƙan da Alhaji Murtala Dan’iya ke yi, musamman tallafa wa marayu, ‘yan gudun hijira da sauran mabukata, inda ta bayyana gudummawar tasa a matsayin abin a yaba.

Majalisar Masarautar Sakkwato ta ce za ta sanar da sabon Dallatun  ranar da za a gudanar da bikin naɗin sarautar nan gaba.

Ana sa ran a naɗa Dallatun tare da sauran sarautu da Sarkin Musulmi ya bayar sama da shekara ɗaya ba a yi bukin naɗin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here