
Alhaji Manir Shu'aibu Fagacin Yabo na farko da aka yi bukin nadinsa a ranar Assabar data gabata lamarin ya kayatar da mutane mahalarta in da kowa ya shiga cikin farinciki da murna yanda aka ajiye sarauta wurinta ba wani coge da zurmugudu.
Fagacin Yabo yanda yake da dimbin jama'a masoya da masu fatar alheri da suka zama silar dagawar martabasa a idon duk wani da ake kira mutum mai hankali da lura, lamarin ya fito a fili ta la'akari da wasu abubuwa uku da suka faru a wurin nada Fagaci wanda ya sanya masu lura suka gane martabar Fagaci ikon Allah ce kawai, duk wanda bai sallama ba wahala ce rabonsa.
Martabar farko da ta faru a wurin mafiyawan mutanen da suka zo bukin nadin sarautar kan Fagaci suka zo ba a fahimci hakan ba sai da aka nada shi a lokacin ne mutane suka fara fita farfajiyar taro, ashe masu nadin sun fahimci hakan za ta iya faruwa shi ne ya sa suka ki nada shi a farko gudun kar nadin sauran takwarorinsa ya zama lami wuri ya zama kufai.
Tashin Fagaci bayan nadi ya mayar da hankalin mahalarta wurinsa gaba daya saboda yanda kamalarsa da martabarsa ta bugi fuskokin jama'a, kai kasan ga mutum da yake da haiba wanda sarauta ta dace da shi.
Tsara bukin sarauta irin na mutunci ya faranta duk wani mai alaka da sarautar ya kuma sanya son Fagaci ganin yanda yake mutum ne mai tsari ba tsallake iyakar al'ada da addini.
Fagacin Yabo yanda ya rike masoya hannu biyu-biyu suka yi masa kara a wurin nadin ta sanya da yawan mutane yin buri su zama kamarsa a wurin rike zumunta domin tana da rana kuma takan yi amfani ne a lokacin da ake bukatarta.