Home Daga Marubutanmu RAUNIN RAYUWA: Fita Ta Biyar

RAUNIN RAYUWA: Fita Ta Biyar

15
0

PAGE 5

A lokacin ta riga ta haɗiye abin bakinta ta yage murya tana faɗar “Kambalastin nan! Yau akwai rikici a gidan nan. Ige! Ige!! Ige!!!” Ta ƙara daga murya tana ƙwalawa kakar tata kira.

ganin cewa kamar ihun banza take yi kakar ba ta jiyo ta ya sa ta ɗaga hannu ta falle Sagira da mari kafin ta sauke hannunta Shafa ta mayar mata da tafi a tare suka dafe kuncinsu ita da Sagira, sai dai sakanni bayan gigitar marin fuskar Sagira ta maye da farinciki tana faɗar “Yauwa yaya Shafa na gode, Allah dai ya biya ki…”

Ita ma ba ta gama rufe bakinta ba Halisa ta cakumi kwalar Shafa suka fara dambe ƙi-ƙi-ƙi-ƙi-ƙa-ƙa-ƙa, da gudu Haifan ɗan shekaru goma ya fice daga sashen ya yi hanyar waje, can bayan mintuna uku sai ga shi sun dawo tare da Ige ta shigo bakinta ɗauke da sallallami a maimakon sallama.

“Innalillahi! Kai me zan gani haka? Ku dakata.”

Tsaye suka yi cak kamar an dakatar da su da masarrafi bayan sun ɗauke hannayensu a jikin juna suna ta haƙi da harare-hararen juna. “Ke ‘yar cakwai me ke faruwa haka ne? Hafan ne ya kirawo ni ya ce ga ku can kuna dambacewa, na ɗauka shiririta ce irin ta yara ashe gaskiyarsa…” Ta ƙarasa faɗa tana kama haɓa.

“Ige wai fa abincin nan da kika ba ni ne suka ɓarar don baƙar hassada tun da na hana su ci.”

“An ɓarar uban wa ya ce ki shigo mana da shi har nan kina mana gadara? Wallahi ko gobe kika kawo sai mun daka masa wawa.” Shafa ta faɗa cikin tsiwa tana kaɗa kai alamun jin masifa.

Ige ta aika wa Shafa mugun kallo tana janye hannun jikarta zuwa gefenta da faɗar “Eh! Za ku aika tabbas, ai ba ma sai an tambaya ba ana ganinku an ga mayunwata. To duk hassadarku dai ‘yar cakwai ta fi ƙarfinku ko  gobe sai kun gan ta da abin da iyayenku ba za su iya sayowa su kawo a ci ba. Ban da ma zalunci ke Shafa ina ‘yar cakwai ina ke, kina nan da zubi kamar wata riƙaƙƙiyar doya? Ko banda ƙarfi ma ai kin girme ta nesa amma don zalunci shi ne kike dambe da ita?. Ba ma laifinki ba ne na waɗannan shashashun iyayen naku ne da suka zauna suka shanya bushasshun ƙafafuwansu kamar sandar rake suna kallo ana zalunci tun da ba ‘yarsu ake zalunta ba shi ne suka yi fatakes kamar ba sa ji.”

Ta nuna ɓangare da maman Shafa, matar baba Sada da sauran matan gidan uku suke zaune sun miƙe ƙafa idonsu ƙyam a kan masu faɗan amma ba wacce ta yi yunƙurin motsawa don raba faɗan a cewarsu; “Jiki magayi, kuma ma duk tsuntsu da ya janyo ruwa ai shi ruwa kan doka.”

Shafa ba ta tamka Ige ba don tana tsoron ta jaza mata babanta ya yi mata tsinannen duka, sai dai ta dinga murguɗa baki tana ƙananun maganganu ciki-ciki. Ige ta tsikaro baki kafin ta gyara zaman kallabinta a kanta ta ja hannun jikarta suka yi hanyar waje tana faɗar “Oho dai ƙaramar mara kunya, ba dai zan daku ba a dake don ko uban yarinya ya yi kaɗan ehe.”

Su ma matan gidan ba wacce ta kula Ige don gudun tado fitina daga baccinta. Da ta zo wucewa ta gabansu ta banka musu harara tana faɗar “An dai yi sakarkarun mata a nan, azzalumai.” Ta yi gaba har a lokacin tana riƙe da hannun jikarta.

Can suka bar farantin Halisa na ta ƙoƙarin ƙwace hannunta ta koma tana matsar ƙwalla amma faɗar take “Kin yi sa’a da ba don Ige ta janye ni ba da na nuna miki ruwa ba sa’an kwando ba ne. Yar banza makaru makaran kawai.”

Sauran ‘yanmatan da ke gefe suka bushe mata da dariya wasu na faɗar “Ko yanzu ai kin daku ba laifi.” Daidai nan suka kammala fita daga ƙofar.
Suna isa sashensu ta fincike hannunta tana ta faman kumbura kamar fulawar da ta sha yeast. “Gaskiya ni Ige kin cuce ni da ba ki bar ni na gama rama wa ba.”

Harara ta aika mata “Ka ji yarinya da cika baki, na ce yanzu gardi nawa ne riƙe da ke da ba za ki iya komawa ki rama ɗin ba?”

Shiru ta yi kamar ruwa ya cinye ta da ta fahimci kakar tata ta harbo jirginta tana so ta ci gaba da borin kunya ba hali don tabbas ta daku da ta ga ta kasa riƙe ƙwallar idanunta sai kawai ta shige ɗakin Ige ta rakaɓe kan gadon ƙarfe mai rumfa da take kwanciya a kai tana kuka mara sauti.

Ta jiyo sautin tsohuwar na faɗar; “Malama da ma kin share hawayen ki taso ga kuɗi ki je ki sayo wani abun ki ci.”

Banza ta yi mata ta yi likimo kamar ba ta ji ba sai kuma Igen duk ta shiga damuwa ta je  ta zauna kusa da ita tana lallaɓa ta, tallaɓo kanta ta yi ta ɗora a cinyarta “Yi haƙuri ‘yar cakwaina, duk zan yi maganinsu tashi ki je ki sayo awara ko kayan shayi ko ma me kike so ki ci kafin a kawo abincin yamma daga gidan babanku Belloti.”

Miƙewa ta yi ta karɓi ɗari biyar ɗin da Ige ke miƙo mata sabuwa gal tana faɗar “Ki kashe duka na ba ki halak malak.”

Ta miƙe cikin murna ko uniform ɗin ba ta cire ba har a lokacin ta fice a hanzarce. Can ma kan hanyar tana tafe tana tsokana idan ta ga ɗan wannan ta bige, idan ta ga wani yaro da kayan wasa a hannu ta ƙwace ta kora shi gida a haka har ta ƙaraci shiriritarta ta dawo gida sai a lokacin ta cire uniform ɗin ta watsar a kan gado, a wannan lokacin ta yi sallar azahar da la’asar.

Kayan ma da ta cire nan ta barbaza su kan shimfiɗa sai Igen ce ta kwashe ta wanke su tas ta shanya a dai-dai lokacin da take shirin zuwa islamiyya wajajen huɗu har da rabi na yamma, lokacin da duk wani ɗalibi mai mayar da hankali ya riga ya kasance a makaranta ita sai a lokacin take shiryawa.

Washe gari da misalin ƙarfe takwas na safe  yaran gidan nasu suka fito shirye a cikin uniform riga da wando kalar purple sai hijabi fari, inda za ka ga banbamci a shigar tasu shi ne a ɗankwalin kansu domin wasu suna sanye da fari wasu kuma kalar purple, wanda hakan ne ke nuna banbanci na matakin karatun nasu, masu farin kallabi su ne seniors ɗayar kalar kuma ta juniors ce, Halisa na ɗaya daga cikin masu sanye da farin kallabin suka rankaya titi a tare.

A ranar ba wacce ta shiga sashen Ige don kiran Halisa sai dai an yi sa’a ta jiyo hayaniyarsu da ma ta gama shiryawa don haka ta bi bayansu ba tare da ta cewa kowa ci kanki ba.

A al’adarsu tare suke tafiya da safe don samun sauƙin abin hawa, amma wurin dawowa sai su dawo a rarrabe saboda kowaccensu tana da tata tawagar da ma masu magana sun ce kowa da kiwon da ya karɓe shi wai maƙocin mai kura ya sayi akuya.

A titin ma sai musayar harara ake tsakanin Halisa da Shafa ba wacce ta yi wa ‘yar’uwarta magana har zuwa lokacin da Hassana ta gama tare abin hawa suka fara ciniki. Sai fama suke da shi a kan ya yarda ya kai su a ɗari-ɗari tun da a haka ma wata kan wata za su yi, tun ba a gama daidaitawa da shi ba Halisa ta shige ta yi bake-bake a seat ɗin baya ganin haka ya sa shafa da Sagira suka ce lallai su ba za su hau wannan adaidaitar ba muddin tare da Halisa za a tafi. Ita kuwa ba ta yi magana ba har a lokacin kuma ba ta fito daga ciki ba, tana so ta nuna musu uban kuturu ma ya yi kaɗan ballantana na makaho. 

Suna cikin wannan hayya-hayyar mai adaidaita ya ce bai amince da cinikin ba dole Halisa ta fito a kunyace. Abokanan faɗan nata suka bushe mata da dariya sai ƙyalƙyalewa suke alamun ta yi musu daɗi.

“Idan kare bai je shi gidan limamai don layyah ba ai ya ƙare a hannun maguzawa.” Cewar Shafa tana ƙara fashewa da dariya ba tare da ta kalli inda Halisa take ba.

Sarai ta san da ita take kawai yau ba ta jin tamkawa ne domin ta lura ya fi matuƙar ciwo ka yi abu don a kula ka a ƙi don haka ta kaɗa kai ta yi gefe ta ja tunga tana faɗar “Tamkawa yabawa ƙyalewa muguwar nakasa…”

Hassana ba ta bi ta kansu ba don duk ta fi su hankali kuma ta lura idan aka daka ta tasu ƙara latti za su yi a kan wanda suka riga suka yi.

Ko da suka isa makarantar sun riga da sun yi latti don a lokacin tara saura kwata shi ya sa ma suka tarar an rufe ƙaramin gate ɗin sai roƙar mai adaidaitar suka yi ya juya da su zuwa babban gate, a can kuma ko da suka ƙarasa an fara taron latti don haka suka joni dandazon ɗaliban da suka tarar a faffaɗan filin wanda a ƙiyasi za su kai su ɗari biyu. Idan ba ka san yawan ɗaliban makarantar ba sai ka rantse fiye da rabinsu ne a filin bayan kuwa a nan wurin ko kwata babu, kaso ma fi tsoka na ɗaliban suna girmama dokar makaranta dalili kenan da ya saka suka kasance a cikin ajinsu a daidai wannan lokaci.

Malamai biyar ne a gun suna kula da ɗalibai da ba su horo ta hanyar saka su tsince ledojin da suka taru a filin makarantar. Suna durƙushe a kan gwuiwoyinsu suna jiran umurni kawai suka ji wata siririyar murya ta ɗalibar da ba su san ko wa ce ce ba ta ce “Mu gudu!.” Kafin ƙyaftawa da bismillah haɗakar ɗaliban da ke gun sun miƙe sun runtuma a guje yuu! Kamar waɗanda aka sakawa gasar tsere.

Wasu daga cikin malamai masu zafin nama tuni suka juya da gudu suka yi gefe gudun a tattaka su. Halisa da take durƙushe kuwa kafin ta yunƙura ta miƙe ta ji ta a ƙasa ana mutsittsika ta tamkar cinnaka, ‘yanmata marasa adadi ne suka yi sunkuwar sallah a kan gadon bayanta.

Ta riga da ta gama sallama rai ga mutuwa kallon abun take kamar a mafarki ta yi bakam tana jiran mala’ikun ɗaukar rai ta ji shiru, can bayan mintuna biyu ta ji komai ya lafa an sararawa takin tsararta da ake yi. Sannu a hankali ta buɗe idanunta sai ta ga tuni kowa ya gama watsewa iya su uku suka rage kwance a ƙasa ita da wata yarinya sai wani ɗan tsamurmurin malaminsu da tsautsayi ya sa ya rasa zafin nama har aka hankaɗe shi ƙasa.

Su duka ukun sai a lokacin suka yunƙura suka miƙe a kunyace,  malamin ya yi hanyar wajen gate ita kuma Halisa ta fara takawa da ƙyar ta nufi cikin makarantar tana tafe tana matsar ƙwalla da buɗe jaka, ta zaro wani ƙyalle a jakar ta jiƙa shi da ‘yan ruwa ta  karkaɗe ƙurar tufafinta. 

Can gefe ta samu wuri ta tsaya ta sauya hijabin jikinta, Allah ya so hijabi biyu take yawo da su da yau ta sha tsokana. Wani zif ta zuge a gefen jakarta ta ciro ɗaya safar ƙafa wankakkiya fara tas ta sauya ta ƙafarta kamar wani abu bai faru ba ta fara takawa cikin ƙarfin hali tana nufar ajinsu. Ba ta so a lura da wani abu ya same ta shi ya sa kawai take juriya amma duk ilahirin jikinta tsami yake yi mata.

Tana shiga ajin Sa’adatu ɗaya yarinyar gidansu da suke aji ɗaya ta kalle ta “Ke kuwa Apsara ina kika maƙale na riga ki zuwa aji?”

Murmushi ta ƙaƙalo ta yi kafin ta ce “Da ke lokacin da kuka gudu ba na gun ina can wurin kai shara babbar bola ko da na dawo na ga duk an watse.”

Zuru kawai ta yi wa Halisa ba don ta yarda da zancenta ba, ita dai gani take kamar akwai abin da ya faru da ita don ta lura kamar jikinta a sanyaye yake haka akwai ‘yar ƙura a jikin wandonta hijabin ma ba shi ba ne wanda suka fito gida tana sanye da shi domin akwai bambancin yadi wancan na farko mai garje ne yanzu kuma mai santsi ne a jikinta.

Wuri Halisa ta nema ta zauna a ajin daidai lokacin da malaminsu mai accounting ya shigo ajin don gabatar da darasinsa.

Da misalin ƙarfe goma na safiya aka kaɗa ƙararrawar tashi break nan da nan ɗalibai suka fara yowar fitar burtu daga rami suna tuttuɗowa cikin filin makarantar. Halima da Halisa ne tafe a jere suna nufar cikin kasuwar makarantar don sayo abin taɓawa.

Halima ta sosa kanta da yake yi mata kaiƙayi don gumi ta kalli Halisa. “Don Allah Apsara ko za ki taimaka kitse mini kan nan idan mun komo daga kasuwa kafin malam ya shigo ajin? Wallahi kaina ƙaiƙayi yake yi mini.”

Har a lokacin jikin Halisa bai daina tsamin murzar da ta sha ɗazu ba amma da ke ba ta so  kowa ya fahimci komai a kai, sai kawai ta gyaɗa kai alamar eh tana murmushi da faɗar “Zan miki mana, kin ji an ce ai naka maganin a zunɗe ka.”

Halima ta yi ‘yar dariya daidai lokacin da ta ja birki gaban robar fanken sayarwa ta ce “Haka ne Apsara tamu, ko an fi ki komai ban da kirki irin wannan.”

Halisa ba ta tamka a zancen ba sai murmushi kawai da ta yi. Siyayyar abubuwan buƙatarsu suka yi suka juya aji da wuri, a cikin class ɗin suka samu ɗalibai da ɗan dama duk sun dawo an barbaje kayan ciye-ciye kan tebura. A can baya suka je suka zauna su ma suna cin nasu a gaggauce. Fatima da ke zaune seat ɗin gaban wanda suke kai ta nuna musu robar da ke cike da kwaɗon shinkafa da rama da ya sha ƙuli da albasa ta ce da su “Bismillanku.”

Halisa ta yi zumbur ta matso ta jefa hannu cikin robar kenan A’isha da suka haɗa kwaɗon tare da Fatiman ta yi saurin riƙe mata hannu. “Malama handamatu jira a ɗan sam miki don na ga alamar idan aka bar ki sai kin handame komai kamar ke kaɗai ce raye a gun nan.”

Tana rufe baki ta ɗauki baƙar ledar da suka juye rama ta ɗebi loma ɗaya ta zuba mata a ledar ta miƙa mata fuska a murtuƙe.

Halisa ba ta yi fushi ba ta amshe tana faɗar “Gado ba na ubanka ba an ba ka allura ina laifi? Hakan ma ya yi, ai dai ko a wutsiya ka mintsini damo ka more masa.”

Ta buɗe ledar tana ‘yar dariya ta hangame baki ta ɗaga ledar ta zazzage shi a ciki.

Bayan sun gama ciye-ciyensu ta karɓi biro a hannun Halima ta zaunar da ita a ƙasan desk ta ciki, ita kuma ta zauna kan bencin zaman ɗalibai ta fara yi mata kitson, ba tsinke shi ne ta dinga yin amfani da biron don fitar da tsagar kitson…

Sun kusa yin rabi kenan aka kaɗa ƙararrawar dawowa aji, duk ɗalibai suka shigo daidai lokacin shi ma malaminsu mai maths ya shigo.
Sanin halin jarabarsa ya sa Halima da ke sunkuye ta ce da Halisa “Apsara mu bar kitson nan har Saƙu baya-baya ya fita, kin san dai halin rashin mutuncinsa idan ya kama mu akwai damuwa.”

Zungure mata kai Halisa ta yi tana faɗar “Ni don Allah sunkuyar da kanki da kyau mu yi maza mu gama, ai ba zai gane ba bari ki ga.”
Ta saki gashin Haliman ta buɗe jakarta ta ciro littafi da biro ta buɗe kamar mai shirin fara rubutu sai kuma ta ci gaba da kitson. Can bayan mintuna uku ta ji an daka mata tsawa. “Hey you! Stand up.” Garin rawar jiki har sai da ta sokewa Halima kai da biron da take mata amfani da shi, ita ma Haliman zabura ta yi ta janyo kan hijabinta ta zura tana tasowa daga ƙarƙashin da take duk suka yi cirko-cirko suna kallon inda suka jiyo sautin tsawar.

ƁANGAREN FATIMA

Da ƙyar ta ja jiki da laluben bango ta isa gun ƙofar ta zare sakatar ta sunkuya nan gun tana mayar da numfashi tare da lumsashe ido. 

Da hanzari ya durƙusa ya tallabo ta yana girgiza kafaɗarta da faɗar “Subhanallahi! Sweetheart me ya same ki haka?.”

Kasa magana ta yi sai ci gaba da ja da sauke numfashi da take yi, nan da nan ya fahimci matsalarta ce ta motsa. Ya rungume ta da kyau a ƙirjinsa ya fita waje da ita don ta sha iska don kuwa ya san zafi ne ya nemi hallaka ta amma da ke kafaffiya ce ta kasa nemawa kanta maslahar fitowa waje ta tsaya fushi.

A hankali yake jan ta tana takawa yana yi mata sannu har suka shiga falon ya kwantar da ita kan doguwar kujerar.

Suna sako ƙafa falon yaya ta miƙe tana faɗar “Subhanallahi! Me ya same ta?”

Cikin muryar tausayawa ya ce “Ina ga rashin lafiyarta ce ta motsa, haka take yi mata dama da zafi da sanyi duk cutar da ita suke har ma gara sanyi da zafin da yake barazanar ɗauke numfashinta.”

“Kai Subhanallahi! Wace rashin lafiya ce haka? A ina ka gano ta ne?” Ta tambaya tana miƙewa ta yo gun da aka shimfiɗe Fatima tana faɗar “Sannu Fati, Allah ya ba ki lafiya.”
Har a lokacin ba ta iya magana sai gyaɗa kai da ta yi alamar ta amsa gaisuwar, a daidai lokacin ne kuma Musa ke fadar “Limoniya ce fa da ita, amma a haka wai kitchen na samo ta cikin zafi bayan ta san illar da yake yi mata.”

“Ayyah! Allah ya ba ta lafiya…” Ta juya idanunta ga Fatima. “Ke ma Fati don Allah ki dinga kiyaye abubuwan da suke tado miki da matsala. Ni zan zo na lallaɓa Allah ya ƙara lafiya. In Sha Allahu zuwa jibi ko ban samu dawowa ba na aiko su Baraka su duba mini jikinki.”

Ta fara nufar ƙofar fita tana faɗar “Kai ma Musa ba zuru za ka yi ba, gobe ka samu ka raka ta asibiti a duba maka lafiyarta. Sai da safenku.”
“In sha Allahu yaya! Allah ya tashe mu lafiya mun gode da ziyara. Ya yi zancen yana bin bayanta don yin rakiya.
Har ƙofar gida ya raka ta sannan ya dawo ciki ya rufe gidan ya koma inda matarsa.

Sabon kuka ya tarar ta tsiri yi nan da nan hankalinsa ya dugunzuma don kuwa yana matuƙar son matarsa, ko yaya ya ga tana kuka tsikar jikinsa tashi take yi, yana kuma sane da idan ba ta haƙura da wannan kukan ba zai iya ja mata jinyar kwana biyu, shi kuma  sam ba zai so haka ba a ‘yan kwanakin nan da yake son su shimfiɗa sabon amarci. Tun da ya tabbatar ba sauran ciki a jikinta ya ƙudurci hakan a ransa ga shi tana neman ɓata masa lissafi don haka ya je gabanta ya tsugunna ya fara aikin rarrashi.

Ya matsa jikin kujerar da take ya zauna a ƙasa yana kama hannunta na dama ya riƙe cikin murya mai taushi ya fara magana.

Haba Teemahna don Allah ki daina wannan kukan, kin san na tsani ganin zubar hawaye a kyawawan idanun nan naki.  Kuma ma duk wannan abu da ya faru ke ce kika ja shi, kin san bana so ana taɓa mini waya saboda halin zargi irin wannan. Yarinyar nan fa ba abin da kike tsammani ba ne…”

Juyo da idanunta ta yi cikin hanzari ta zuba masa su, wanda hakan ke ƙara narkar da shi ta ce “Ba abin da nake tsammani ba ne to me ne ne? Marina fa ka yi a kanta.”

Ɗayan hannunsa ya ɗora kan ɗayan ya ƙara matse hannunta da ke  tsakankanin nasan yana yi mata kallon cikin ido. 

“Raina ne ya ɓaci saboda kin yi mini kafiya, amma don Allah ki yi haƙuri komai ya wuce kamar ba a yi ba kin ji sweetheart.”

Sannu a hankali ta zare hannunta a jikin nasa ta yunƙura ta miƙe zaune ta kafe shi da idanu, kallo mai cike da ma’anoni wanda ko ba a faɗa maka ba kasan akwai zantuka masu tarin yawa da nauyi da suke danne zuciyarta har suka kasa furzuwa.

Ummu Inteesar ce

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here