Na
Ruƙayya Ibrahim Lawal (Ummu Intisar)
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
PP 17
Wata dabara ce ta faɗo mata a rai ta yi sauri ta zauna kan kujerar da ta tashi tana ci gaba da aikinta sannu a hankali tana rera waƙoƙin Larabci da aka koya musu a islamiyya, wasu ma tun suna yara.
Da sallamarsa ya shigo gidan bayan uwar ta yi masa umurnin hakan da ta leƙa wajen ya tsugunna a nan gaban murhun yana gaishe da uwar.
Har cikin ranta tsoronsa ya gama narkewa ji take kamar za ta sake fitsari a wando sai kuma ta kanne ta ƙara ɗaga murya cikin shauƙi tana ci gaba da rera waƙa kamar haka:
“Wa li ummi kulli fadlin fa hiya hairul ummuhati, hamalat ni arda’at ni hiya ruhi wa hayatı.”
Ta dage tana maimaita baitin cikin salo daban-daban na shauƙi. Dariya kawai ya yi a zuciyarsa don kuwa ya fahimci manufarta, tana so ta yi amfani da waɗannan baitukan ta yaudare zuciyarsa ya fasa yi mata hukuncin da ya yi niyya.
Sai dai idan ma ya ɗaga mata ƙafa wannan karon a gaba za ta yi abin da ya fi waɗannan ɗin, shi ko ice tun yana ɗanye ake tanƙwara shi idan ya bushe ba ya tanƙwaruwa sai dai ya karye.
Yana gama gaishe da mama ta dago kanta cikin ƙarfin gwuiwar da ta ara ta yafa. “Sannu da zuwa yayanmu.” Ta faɗa cikin salon son ɓoye firgicin zuciyarta amma ta gagara yin hakan domin sai da yanayin tsoro ya bayyana a muryar tata.
Miƙewa ya yi bai ce mata uffan ba ya zaga bayan ɗakin mama kan rufin wani tsoho kuma ƙaramin ɗakin ajiye-ajiye da ke gun yana laluben abin duka, can ya ga busassun bulolin itace a saman ɗauko ya ɓoye su a bayansa ya fito.
Ta bayanta ya sallallaɓo ya zuba mata gezar har sau uku a jere ba ƙaƙƙautawa ta zuba ihu ta miƙe tare da sakin rigar mama da ke hannunta ta fara soshe-soshen baya da hannun mai kumfa.
“Na shigangaɗina, me na yi ni jikar mutum huɗu?”
Ko a yanzu ta so da ta ba shi dariya yanayin yadda ta furta zancen cikin manyance kamar wata tsohuwa, dake ita ai ba a raba ta da kilinkison magana da iya faɗi tamkar cirarren sarki ba.
Dagewa ya yi yana ci gaba da zuba mata ta fita da gudu ta yi cikin ɗakin maman ya bi ta har falon yana zane ta sai da ya ga da gaske zai illata ta don har shatin bulalin sun kwanta mata a gefen fuska da hannu, ga ihun da take ta dafe gefen idonta ko da ta janye hannun idon ya yi ajin jini a cikin ƙwayar ga wani rauni a gaf da idon nata ta gefe.
Bulalin da suka kakkarye ya watsar sauran lafiyayyar ya riƙe ta a hannunsa yana huci.
“Gobe ma kya ƙara. Ba ma a iya nan layin ba, in sake jin kina tafe kina ciye-ciye a hanya ko zubar mana mutunci irin wanda kika saba. Idan na kama ki za ki ga yadda zan sauya miki kamanni.”
Cikin ƙunƙuni ta fara magana can ƙasan maƙoshi “Allah ya isana wallahi, kawai don ka ga ana tsoronka sai ka tasam ma zalunci? Mugu kawai macijin sari ka noƙe.”
Har ya juya ya jiyo guna-guninta don haka ya sake waigawa ya kalle ta ran nan haɗe tamkar jagaban ‘yan wuta.
“Me kika ce?”
“Ba komai cewa na yi Allah ya yi maka albarka ya shirya zuriya ta hanyar lalaci…”
Ta ƙarashe furucin da ragaggen sauti sosai, duk da hakan sai da kunnensa ya jiye masa me ta faɗa ya dai ƙyale ta ne saboda ya lura yawan sa mata hannu yana shirin fanɗarar da ita ta daina tsoronsa tun da har ga shi ta fara maida masa da martani abin da a da sam ba ta iya yi.
Ya fice daga ɗakin a sanyaye yana kitsawa a ransa dole zai canza mata hanyar hukunci dabam da wannan, zai dai zurfafa tunani a kai gudun haihuwar ɗa mara ido.
Bayan ta gama kukanta kuma haka mama ta tilas ta mata ƙarasa wankin da ta faro.
Duk lokacin da ta sanya hannunta cikin ruwan kumfan tana jin wani raɗaɗi na musamman yana ratsa ta ta hanyar shigar sinadarin wankin cikin raunin bulalar da ya fasa mata wani ɓangare na bayan tafin hannun nata.
Tana yi tana matsar ƙwalla har ta kammala, da ma ta ƙagu ta gama ta koma in da tafi wayo, inda ake ririta ta wurin da komai ta yi daidai ne.
Gama shanya kayan kedawuya ta ce da mamanta ita za ta tafi. Maman ta kalle ta fuska ba yabo ba fallasa “Ki ɗauki abincinki ga shi can ki ci, kafin ki je ki ɗorar a gun kakarki cewa na hana ki abinci.”
Zama ta yi ta ci abincin domin ko da yunwa sosai a cikinta, tun ƙarin kumallo ba ta sake saka abin kirki a cikinta ba sai yanzu. Da ta kammala ta miƙe ta wanko hannu ta sanya hijabinta ta yi bankwana da maman.
Ko da ta fito dabar yamma ta matasa da take taruwa a kusa da gidan maman sun gama haɗuwa, mazaje ne ga sunan dandazo-dandazo. Matasan ma’aurata sun yi tasu dabar samari sun haɗa ta su dabam. Sai yara ‘yan maza da mata da suke ta wasanni a gefe, kowa dai yana sabgar gabansa ta wuce su ta nufi hanyar titi jiki duk tsami.
Wani ƙaramin lungu ta bi don ta kaucewa idanun mutane da ta lura suna ta bin ta da ido, wasu suna yi mata kallon tausayawa wasu na mamaki. Tagwayen tsaki ta ja tana ƙara saurin tafiyarta.
Da a ce ta san abin da za ta tarar a wannan lungu da ta zaɓi ta miƙe hanyarta samɓal har titi, don kuwa ta yi gudun gara ne ta faɗa gidan zago.
Ta yi nisa a cikin layin ta tarar da dandazon samari sun yi dabar da ta fi wacce ta gujewa yawa ga shi ba damar komawa baya don haka ta ja dogon tsaki da ya fi na baya sauti cikin ƙuncin rai ta fara takawa da sauri-sauri a ranta tana faɗar ‘Aikin banza kawai, kun wani zauna kuna ƙarewa mutane kallo har sai kun ga muninsu.’ Ta janyo hijabinta tana kare fuskarta da take a kumbure don ba ta so a gano an dake ta ne.
Ba ta san ya aka fara ba sai jin ta ta yi ƙasa rikicaa goshinta ya ƙumu da wani dutse mai tsini da yake kafe cikin ƙasa, ‘yar ƙara ta sake a daidai lokacin da take yunƙurin tasowa, tana jin lokacin da wasu daga ‘yan cikin majalisar suke furta “Subhanallahi! Sannu ‘yanmata.” Wasu kuma suna haɗa baki wurin faɗar “Miƙe yanmata.”
Wasu yara daga gefe kuma suna dariyar murna cike da ƙuruciya. “Laa! Ta ci ƙasa.”
Takaici fal cikinta ta yi dabarar miƙewa, tana gama daidaituwa a tsaye ta fara ƙoƙarin ci gaba da tafiya sai ta ji ƙafarta na cijewa alamar ta ji ciwo a inda ya bugu. A sa’in ne kuma ta tsinto wata matashiyar muryar namiji tana furta “Sannu ‘yanmata bi a hankali! Ina ga kin ji ciwo fa.”
Ba ta juya ba kawai ta ci gaba da takawa a kunyace tana yi masa godiya don ko ba komai wanda ya yi maka sannu ya fiye maka wanda ya yi maka dariya a yayin da wata masifa ta afka maka.
Ganin dai da gaske ba za ta iya ci gaba da tafiyar ba sai cije leɓe take tana ƙoƙarin takawar ta ƙarfin tsiya amma ƙafar ta yi gardama, hakan ya sa shi cewa “Idan ba damuwa bari na ɗauko mashin ɗina na sauke ki a gida.”
Bai jira jin me za ta ce ba ya juya a gaggauce ya janyo abin hawansa da ke fake a gefen majalisar ya gangaro da shi inda take tsaye yana furta “Bismillah hau mu je.”
Juyowar da za ta yi haka suka haɗa ido su duka kowa ya ɗan fito da ido waje suka ƙame a gun kamar an dasa su, wani irin kallo suke watsawa juna wanda yake da bambancin ma’ana a duka ɓangare biyun.
“Ke ce a nan?” Ya jefa mata tambaya.
ƁANGAREN FATIMA
Ba ta da zaɓi face ta aikata abin da ya umurce ta don haka ta je ta yi gwajin fitsarin ta fito ta tarar da shi a ƙofar banɗakin nata na ciki da alama ya kasa jiran ta a falo shi ya sa ya zo nan ya kasa ya tsare. Tana jefo ƙafarta waje suka haɗa ido ta yi saurin yin ƙasa da kanta tana miƙa masa tsinken, a yanzu dai ba ta ji za ta jure kallon cikin ƙwayar idonsa don wani ƙaramin dodo ta ga ya koma mata lokaci ɗaya.
Fisgewa ya yi da ƙarfi ya tsayar da idonsa ƙyam a kan wurin alamar, kamar dai yadda ya yi tsammani haka ya gani don haka a take ya ji sabuwar tsanarta ta yi masa dirar mikiya a zuciya. Ya so wannan hutun na yau ya same su cikin kyakkyawan yanayi shi da matarsa domin ya ci buri sosai a kan more hutunsa na yau ta hanyar ba wa iyalinsa cikakkiyar kulawa da nuna tsantsar ƙauna amma ga abin da ya faru.
Kasa yin magana ya yi domin kuwa muddin ya ce zai yi furuci a yanda yake jin zuciyarsa matsala za a samu. A take ya ji ya tsani tsayuwa ma a kusa da ita ya fice a zuciye zuwa falo ya tattara laptop da duka takardun da yake aiki da su ya koma ɗakin gadonsa ya rufe ta ciki.
Ita kuwa ta jima a cikin ɗakinta zaune a ƙasa tana ta zullumi da tunanin fita, ita da falonta amma tana shakkar zuwa can. Haka ta wanzu har bayan mintuna 30 sannan ta yi ƙarfin hali ta miƙe, wata muguwar yunwa take ji kamar an yashe kayan cikin nata, ga shi ma yau ko karin kirki ba ta yi ba don ko da suka zo breakfast sai da ta ga ya dage sannan ta sa ruwan tea a cikin nata tana gama shanyewa ta ji cikin na hautsinawa ta yi ciki da hanzari saboda gudun ya ɗago halin da take ciki.
Ko bayan da ta gama haras da abin da ke cikinta ba ta yi gaggawar fitowa ba sai da ta dawo hayyacinta ta feso turaruka masu sanyin ƙamshi da ba za su dame ta ba sannan ta fito ta same shi.
Sanin yunwa ba ta da hankali ga kuma lalurar da take ɗauke da ita a gaggauce ta nufi kitchen ta ɗora farar taliya da manja, ta duba robar da take ajiye yaji ta samu ragowar yajin daddawa mai haɗe da gauta ta ciro faranti ta shaƙo shi da farar taliyar ta juye soyayyen manjan ta a wata ‘yar aljanar roba ta rakito kayan bayan ta sako dungulen maggi biyu a kai ta nufo falo.
A nan kan carpet ta barbaje hajar tata ta tsalala uban mai da yaji mai yawa ta fara ci hannu baka hannu ƙwarya kamar wani ne zai ƙwace mata. Daidai lokacin ya fito ya watsa mata kallon uku saura kwata ya janye idanunsa cike da haushi ya bi ƙofar fita falon yana faɗar “Zan fita ki tabbatar kafin na dawo kin girka mini tuwon masara da miyar yauƙi.”
Iya abin da ya faɗa kenan ya fice zuwa ƙofar gida inda ɗaya daga cikin abokan aikinsa na jami’a Sudais yake jiran sa. A soro ya tsaya ya lalubo nutsuwa da fara’a ya ara ya yafa domin ɓoye sirrin gidansa sa’annan ya ƙarasa gun shi.
A ciki kuwa inda ta kammala cin abincin a nan bacci mai daɗin yanayi ya yi awon gaba da ita, ta ɓingire ba tare da wanke hannu ba tana jin yadda iskar fankar saman ke ratsa ta da kyau.
Ya jima sosai a waje fiye da awa ɗaya da rabi suna zaune a mota suna tattauna wani issue mai muhimmanci na department ɗinsu a ƙarshe suka ɓige da ci gaba da marking takardun c.a ɗin. Sai wuraren 1:30 na rana suka yi sallama da juna Sudais ya ja motarsa ya fice shi kuwa Musa ya dawo ciki rungume da tashi na’urar a hannu ɗaya kuma yana riƙe da fararen takardu.
Yana sako ƙafa cikin falon ya ƙame yana ƙare masa kallo daga kowacce kusurwa, can camerar idonsa ta sauka a tsakiyar falon inda ya hango ta yashe a gefen kwanon abincin da ƙudaje ke bin wanda ya watse a ƙasa da ragowar na cikin farantin. Garin mirgene-mirgene ma ta kifar da robar manjan da yake a buɗe kan milk carpet ɗin, har ma ta mirgina ciki ya ɓata mata dogon wando milk ɗin da take sanye da shi.
A nan take haushin da ya ji ya fara yi masa adabo ya sake yi masa dirar mikiya. ‘Lallai wannan yarinyar ta raina ni, in saka ta aiki ta baje baki tana bacci?’
Nan take ya ji ya zo iya wuya, a hasale ya saka ƙafa ya yi mata kyakkyawan shurin da idan dai ba baccin mutuwa take yi ba dole ta farka.
Firgigit ta yi ta buɗe ido ta miƙe zaune tana faɗar “Eyyeah! Me ka ce?”
Ya yaɓa mata kallon wulaƙanci “Sannu hamshaƙiya mandiyya masu zuwa Makkah da buhun ƙuli. Ke da na ce ki yi mini tuwo kafin na shigo shi ne kike ta bacci?”
Kafin ya rufe baki tuni ta miƙe tsaye tana fito da ido alamun ta tuna, ta fara ƙoƙarin ficewa daga falon tana faɗar “Am! Don Allah yi haƙuri yanzu zan je na ɗora, wallahi bacci ne ya sure ni.”
Ta fara takawa da sauri ya dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa “Ke!”
Ta ƙame a gun. “Wane shegen ne zai gyara miki ɗakin? Tun wuri ki mayar da hankalinki mazauninsa ba zan ɗauki ƙazanta ba.”
Ita sai ma a lokacin ta ga yanda ɗakin ya yi ta dafe goshi a hankali take furta “Ya Salam!”
Bai zauna a falon ba kamar yadda ya yi niyya sai ya wuce ciki kawai ya ajiye kayan aikinsa da ya shigo da su ya ɗoro arwalla ya fito sanye da farar jallabiya da hula taɓe ni ka sha hadisi riƙe da carbi a hannunsa ya fice daga gidan duk ransa ba ya masa daɗi.
UMMU INTISAR CE




