Home Daga Marubutanmu RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 15

RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 15

21
0

NA

Ruƙayya Ibrahim Lawal (Ummu Intisar)

PP 15

ƁANGAREN FATIMA 

Da ƙwarin gwuiwarsa ya koma ɗakin taron kamar komai bai faru ba suka ci gaba da shagulgulan biki. Ko da Hanifa ta tambaye shi ina Fatima kuwa? Sai ya ce “Tana mota kanta ne ya matsa mata da ciwo shi ne na raka ta ta kwanta kafin a kammala taron.”

Daga haka ba wanda ya ƙara tambayarsa a game da ita har aka tashi taron. A tare da abokan nasa duka suka fito, Hanifah da sauran matan suka ce za su je mota su yi wa Fatima sannu kafin su wuce. Mazajensu ba su hana su ba suka yi zaman jiransu a mota su kuma suka je a tawaga ɗaya har ƙofar motar Musa.

Shi kuwa tun da ya ji sun furta zancen ya yi hanzarin shigewa gaba yana matsawa kusa ya danna remote na motar don yin unlocking. Tana kwance a motar cike da haushi har bacci ya fara sace ta ta ji ƙarar motar alamar an danna masarrafinta  daga waje. Da hanzari ta tashi zaune tana ƙara tamke fuska yadda ba zai ga alamun rahama a fuskar tata ba ballantana ya yi tunanin neman yafiya.

Har aka buɗe ƙofar ba ta yi magana ba kuma ba ta waigo ba sai da ta ji muryar mace a kunnenta sannan ta ɗago da sauri ta kai dubanta inda ta ji sautin.

“Fatima ya jikin naki kuwa?” Ta yi sama da ido ta dawo da shi kan Hanifah alamar neman ƙarin bayani. Ganin haka Hanifah ta ɗora da “Ashe ba ki ji daɗi ba kina ta fama da ciwon kai shi ya sa muka neme ki muka rasa.”

Yaƙe ta yi tana ta kalato busasshen murmushi don ta yi abu ya faskara sai “Um!” Kawai ta furta a ranta tana al’ajabin ƙaryar da ya zabga don ya ba wa kansa kariya.

Fatan samun sauƙi ta yi mata ta juya tana faɗar “To mu za mu wuce, Allah ya daɗa sauƙi.”

Haka duk sauran matan suka dinga leƙawa ta wundon ƙyauren motar suna gaishe ta shi ko gogan yana hakimce a gaban mota har suka gama ‘yan gaishe-gaishen nasu suka tafi.
Ta harari bayan ƙeyarsa a ranta tana cewa  ‘Oh! Abin da ka shirya musu kenan?’ Uffan bai ce ba ya ja motar suka nufi gida don har a lokacin bai huce daga abin da ta yi masa ba, ya dai jure ne har su koma gida don kar su raba hali a cikin jama’a. Abin kunyar a kansa zai ƙare don shi ne zai kifar da ɗan ragowar mutuncin nasa a idon jama’a.

Suna isa ya faka a ƙofar gidan ba ta ko kalli inda yake ba ta buɗe gidan bayan ta fito ta yi ciki ranta ba daɗi.

Ya kulle motar a garejin ta ciki ya zaga ya rufe ƙofar gidan ya nufi ciki. Kasancewar da ‘yar tazara tsakanin ƙofar gidan da ɗakin taku bibbiyu ya dinga haɗawa don ya yi hanzarin isa inda yake muradi.

A falo ya tarar da ita ta cire kallabin tana shirin shigewa uwar ɗakan ya yi tsalle uku daga inda yake ya damƙo hannunta ta baya da ƙarfi ya janyo shi sai kuma ya saki yana sauke huci. Sosai ta tangaɗa har saura kaɗan ta ci ƙasa Allah ya ba ta iko ta kama bango ta dafe.

Kallo mai cike da ma’anoni take aika masa amma ta kasa yin magana ma a zuciyarta take raya cewa ‘Ba ita ce ya kamata ta yi fushi ba ita da ya ci wa zarafi ya ajiye ta a cikin zafin mota tsawon awa ɗaya da rabi?’

Kafin ta ƙarasa zancen zuci ta tsinto muryarsa a fusace yana faɗar “Ni za ki tozarta a cikin dandazon al’umma? To wallahi bari ki ji in faɗa miki ba ki isa ba. Ban auro wannan matar ba kuma ba zan taɓa ajiye irin ta a gidana ba.”

Ganin irin kallon sake da bakin da take yi masa kamar ba ta san me ta aikata ba ya sa ya iya karanto zuciyarta mai cike da neman ƙarin bayani kafin ma ya kai ga magana ya jiyo ta tana faɗar “Me na yi maka?” Yana ta faman sauke huci kamar kumurci ya ce da ita  “Au! Ba ma ki san me kika yi ba? Gaskiya Fatima kin cika ‘yar rainin hankali. Wai tsaya ma in tambaye ki shin na biya sadakinki ko zaman dadiro muke yi?”

Ba ta iya ba shi amsa ba sai ci gaba da kallon shi da take yi, ya daka mata tsawa yana maimaita tambayarsa. Zahirin gaskiya ta tsorata a lokacin don tashi ɗaya ta ga ya rikiɗe mata daga masoyi zuwa mugun dodo. Murya na sarƙewa ta amsa a hankali “Ka… Ka biya.”

Matso ta ya yi ta fara ja da baya har sai da ta ji bayan nata ya haɗe da bango tukunna ta haƙura, ya ci gaba da matsotan sosai har suna jin numfashin juna “Idan har haka ne me ya sa kike kunyar bayyanar da hakan? Sona kika daina yi ko ƙyamata kika fara yi da har don na riƙe hannunki za ki tozarta ni cikin abokanai? Su haka kika ga matansu sun yi?”

Yanzu ta fahimci matsalar don haka ta yi ƙasa da kai tana ba daɗi a ranta, da murya mai nuna tsantsar nadama ta furta “Don Allah ka yi haƙuri yaya wallahi kunya ce ta sa na aikata hakan.”

“In yi haƙuri? Haƙuri dai haƙuri kullum haƙuri?” To ki sani ni wannan kunyar taki wallahi tana matuƙar cutar da ni. Na yi ta yi miki haskiya kan hakan ba ki fahimta ba, na miki kara nan ma ba ki gane ba. To a yanzu haƙurina ya zo ƙarshe sai dai ki zaɓi tsakanin kunyar ko aurenki duk wanda kika fi so domin ni ba zan ci gaba da zaman cutuwa ba. Haƙurin shekara huɗu da ɗoriya ma da na yi Allah ya bada lada. Idan kuma kin fi so na ƙaro miki abokiyar zama ne sai ki faɗa.”

Ganin ya ɗauki tururi sosai a kan ɗan wannan abun ya saka ta  durƙusawa kan gwuiwoyinta ta ba shi haƙuri tare da yi masa alƙawarin za ta dage ta koyi yadda za ta zauna da shi kamar yadda ta yi a baya domin kuwa ba ƙaramin ɗaga mata hankali zancen ƙarin auren nasa ya yi ba.

Bai ce komai ba ya juya zuwa ɗakinsa har a lokacin zuciyarsa na tafarfasa. 

Ita kuwa sai ta miƙe tana mayar da ajiyar zuciya ta shige uwar ɗakan ta zauna kan dressing mirrow tana kallon yadda firgicin ɗan lokaci ya fara sauya mata kamanni.

Ta sani ya yi matuƙar haƙuri da ita a baya irin wanda masoyin gaske ne kaɗai zai iya, tana tuna lokacin da aka kawo ta gidan nan a matsayin amarya ko zama kusa da shi ba ta iya yi saboda tsananin kunya.

Idan ma shi ya zauna ta shi take ta sauya gun zama, a ranar farkonta ma sai haƙura ya yi ya kwana a falo ya bar mata gadon saboda yadda ya ga ta ɗaga hankalinta sai da ya yi da gaske ya samu kanta har take iya kaɗaicewa da shi, amma fa tun daga wancan lokacin har izuwa yanzu ba ta iya cin abinci kwano ɗaya da shi ba kuma don ƙyama ba sai don kunya, ko ɗan irin sunan soyayyar nan da mataye ke faɗawa mazajensu ta kasa furta masa ko da sau ɗaya ne, kullum sai dai yaya.

An sani cewa kunya halitta ce kuma ado ga ‘ya mace amma ita tata kalar kunyar ta zarce ƙa’idar hankali.

“Idan kuma kin fi so na ƙaro miki abokiyar zama ne ki sai ki faɗa.” Zancensa ya shiga dawo mata yana yi mata amma kuwa, nan da nan zuciyarta ta fara yi mata zafi sosai, ta tsani kalmar kishiya, a kan tsananin kishinta ko yaran maƙota da suke zuwa taya ta aiki da hira yana shigowa za ta sallame su saboda mace ta kalle shi ko shi ya kalle ta babban zunubi ne a duniyarta. ‘Yanzu ya za ta yi kenan? Anyah za ta iya cika kalamanta na gyarawa ko ta furta ne kawai?’

Haka ta shafe dogon lokaci cikin nazari da tunane-tunane har ta samarwa kanta mafitar za ta cije ta gyara matsalarta ko don gudun ta afka wata fitinar a gaba.

Da dare ta lallaɓa ta je ta samu mijinta suka yi sulhu komai ya wuce kamar ba a yi ba.

Bayan watanni biyu ciki ya sake bayyana a jikin Fatima ta yi matuƙar farinciki sosai cike da fatan ganin jininta a duniya ta kuɗurce ko me za a yi ba za ta bari ta rasa shi ta hanyar ganganci ba.

Sanin halin mijinta ya sa ta kuɗurci ɓoye masa wannan al’amari  har zuwa lokacin da zai yi ƙwarin da ba zai iya cutar da shi ba sai dai ta fara fuskantar cewa wannan cikin ba lallai ya ba ta haɗin kai ta cika muradinta ba domin mai yawan laulayi ne.

Da ƙyar ma ta iya jure ɓoye hakan na kwana biyu daga ranar da ya fara ba ta alamu shi ma sa’ar da ta yi tun tara na kowacce safiyar ranar aiki yake fita ba ya dawowa sai biyar ko shida na yamma, nan ma abinci kawai yake ci ya kimtsa ya zaga gidan mahaifiyarsa da yake unguwar da ke makwabtaka da tasu, a can yake zaman hirar majalisa ba ya nufo gida sai taran dare ranar da ya jima ya kai goma.

Sai ta al’adantawa kanta shan magungunan da suke dakatar da amai ko tashin zuciya, ta kan yi ƙoƙari kuma ta girka kalar abincin da take iya ci ta adana gudun kada ya ɗora mata ayar tambaya. Idan an zo cin abinci sai ta fake da ai ta ci nata kafin ya dawo.

To a washegarin rana ta uku ya kama ranar Larabar da ta kasance ɗaya daga cikin ranakun gama-garin hutu (public holiday)

Tana zaune a falo wuraren ƙarfe 11 na safe ya fito daga shi sai singileti da dogon wando jeans ya zauna a kujerar zaman mutum biyu da take kai ya fara daddanna laptop ɗinsa yana shirya jadawalin makin ɗalibansa na aikin gida da ya bayar a matsayin c.a.

Iskar da take shigowa daga waje ta buso mata ƙamshin turaren da ya saka zuwa hancinta, nan da nan zuciyarta ta fara tashi sai ta ji tana yunƙurin amai. Ta yi saurin toshe hancin nata ta miƙe da gudu ta nufi toilet ɗin waje da ya fi kusa da ita a lokacin.

Sosai ta ke sheƙa amai kamar za ta zubar da kayan cikinta, mintuna biyu suka shuɗe da ita a cikin wannan halin kafin ta dawo hayyacinta. Ta buɗe famfon da ke ciki ta tara ruwa a buta ta sheƙawa fuskarta da wuyanta. Ta wanke bakinta sosai sa’annan ta saka tsintsiya da ruwa ta wanke gurin tas ta ɗago tana sauke ajiyar zuciya da dafe saitin ƙirjinta tana juyo da nufin fita.

Juyowar tata kedawuya ta gan shi tsaye a kanta yana jefa mata kallon tuhuma, so take ya ɗauke idanunsa a kan fuskarta kafin ya karanto yanayin da take ciki, amma sam ya ƙi yin hakan.

“Lafiyanki kuwa?” Ya tambaya har sa’in bai janye idon nasa a kanta ba.

Ta raɓa ta gefen shi tana wucewa yayin ta fara magana cikin ƙwarin gwuiwa “Ba komai, kawai ɗan ƙaramin tashin zuciya ne.”

“Me ya janyo tashin zuciyar?” Ya bi bayanta yana ƙara jefa mata tambayar da ke sake dulmiyar da ita cikin fargaba.

“Hancina ne ya zuƙo wari mara daɗi daga waje.” Ta amsa tana yin shigewarta ciki.

Fuskar nan a haɗe murtuk ya bi bayanta, sai dai bai koma ya zauna kamar yadda ya kamata ya yi ba, ɗakinsa ya shiga ya fito yana miƙo mata wani ɗan farin tsinke.

Kallon shi ta yi da alamun ruɗani a fuskarta “me zan yi da shi?”

Harara ya banka mata wacce tasa ba shiri ta yi ƙasa da kanta. “Ina ce kin fi ni sanin amfaninsa? Malama maza ki je ki gwada ina jiranki a nan.”

Ya nuna mata ƙofar bedroom, tashin hankalin da ya ziyarce ta ya hana mata ko da motsa ɗan yatsar ƙafatarta har sai da ta ji yo sautin muryarsa cikin ƙaraji yana daka mata tsawa “I Said use the door! Ba na buƙatar ɓata lokaci.”

Jiki na rawa kamar ana kaɗa ta da mazari ta shige ciki, haƙiƙa a irin waɗannan lokutan a baya ya sha yi mata tsawa, amma ba ta taɓa jin ta cikin yanayin razana irin na yau ba. ‘Wannan karon ko waɗanne nau’ukan wulaƙanci da uƙuba za ta fuskanta?’ Wannan tunanin ne ya bijiro mata a zuciya ya hana ta sukuni.

ƁANGAREN SURAYYAH

“Tsarki ya tabbata ga Mahaliccin wannan kyakkyawar sura ma’abociyar kwarjini.” Ya furta cikin sassanyar muryarsa mai daddaɗan amo.

Bargon kunya ta ji ya lulluɓe ta sai ta sake sadda kai ƙasa.

“Sunana Ahmad Ashir ni mazaunin unguwar Sunusi ne, abin da yake tafe da ni gunki buɗaɗɗen saƙo ne daga zuciya mai riƙe da ƙoƙon bara zuwa ga zuciyar da ake nema daga gare ta. Ina fatan ko ba zan samu komai ba zan samu martanin soyayya da ƙauna, dama ɗaya za ki ba ni ni kuma zan yi amfani da ita na mayar da ke mallakina kuma sarauniyata har abada.”

Ba ta ɗago ba haka nan ba ta ce uffan ba, sai dai daga fara zancensa zuwa kashe sakar zarensa ta yi murmushi ya fi sau shurin masaƙi.

Shi ne ya sake cewa “Kin bar ni ina ta zuba ni kaɗai kamar ‘ya’yan kanya.”
‘Yar dariya ta yi kafin ta ce “Ni kuma Surayyah Shu’aibu, na kammala karatun NCE na fannin primary Education kuma ina zuwa islamiyya na karanta littafan sani da ɗan dama.”
A daidai lokacin Salman ɗan shekaru sha biyu ya shigo ɗakin riƙe da farantin zamani ɗan madaidaici da yake ɗauke da kwalin lemon 5alive biyu da robar ruwa ɗaya sai glass cup guda biyu ya ajiye yana faɗar “Uncle wai ga abin sha in ji mommy.”
Albarka ya sakawa yaron sannan ya fice daga ɗakin, yana ganin ficewarsa ya mayar da hankalinsa kanta.

“Madallah hakan ya yi kyau. Na so in manta, duk fa wannan kyaun naki ne ya ruɗe ni ban sanar miki aikina ba. A yanzu haka ni jami’in civil defense ne da nake a ƙaramin matsayi. Kuma ina da sana’ar yi don kuwa ƙwararren telan mata ne ba alfahari ba a lokutan da kasuwar ɗinki ba ta garawa kuwa na kan je ɗan ƙaramin shagon provision da nake da shi a unguwarmu na zauna. To ina ga ko a yanzu hidimar auren ta tashi alhamdulillah zan iya riƙe iyali.”

Ta ji matuƙar daɗi a ranta har ta ji cewa da dukkanin alamu lokacin yankewar wahalarta ne ya zo. Ta samu wanda zai ɗauke ta daga inuwar su Mama zuwa tasa inuwar da take fatan ta samu kwanciyar hankali da nutsuwa fiye da gidan mahaifinta.

A haka suka ci gaba da tattaunawa na ɗan wani taƙaitaccen lokaci sannan suka yi sallama da juna bayan sun yi exchanging number juna, da zai tafi ya kawo dubu goma ya ba ta ta ƙi karɓa sai ya ajiye mata su nan a kan table ɗin da aka ɗora musu abin sha a kai ya fice daga ɗakin.

Can jimawa kaɗan da fitarsa sai ga anty Atika ta dawo ɗakin ta tarar har ta miƙe da nufin fita ita ma. Ta nuna mata abin da ya bayar, “Masha Allah! Ai ko kin gode, da ma shi in dai kyauta ce ba na jinsa. yanzu gida za ki tafi kenan?”

Ta amsa mata da eh sannan ta nunawa anti Atikar ta yi duk yadda ya dace da kuɗin, da dai ta ga lallai ilalla ba za ta karɓi kuɗin ko da wani abu daga cikinsa ba haka ta haƙura ta kwashe ta zuba su a jaka cikin jin kunya da tunanin wa ce kyautatawa ya kamata ta yi wa antin da kuɗin amma a fakaice.

Da ta ƙarasa gida ta miƙa wa mama kuɗin duka ta ce ta yi yadda ta ga ya dace sai dai ba ta ɓoye mata ƙudirinta na kyautatawa yaran Atikar ba. Mama ma ta amince da shawarar don haka ta ware dubu uku ta bayar aka yi musu sayayyar kayan ƙwalam da za su iya amfani da shi wurin zuwa makaranta. Ita kuma maman ta ɗauki dubu biyu don tasa albarka. A cikin natan ta samma A’ishatu ɗari biyar.

Duk da Surayyah ba ta hassadar ƙanwar tata amma sai da ta ji haushin hakan da mama ta yi, ta ga ai ita nan take samun nata kuɗaɗen a hannun samari amma ko ƙwandala ba a sam mata a ciki sai abin da A’ishatun ta yi nufi don kanta, amma ita ko dubu ɗaya ta samu daga waje in sha Allahu sai maman ta roƙe ta a kan ta kyautatawa ‘yar’uwata ta tsakurar mata wani abu daga ciki. Yau ma ta yi mamakin ganin mahaifiyar tasu ba ta ɗauki ɓangare ba kamar yadda ta saba kuma ba ta yi mata roƙon da ta saba yi mata ba a duk sanda irin wannan ta samu.

Ummu Intisar ce

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here