Sallah mai yawan ƙawa(ado) a cewar Bahashe, saboda a bukukuwan Sallah suna ƙayatarwa ne kan farinciki da kwalliya da al’ummar musulmi ke yi, a ci abinci, a je masallacin idi, a ziyarci ‘yan uwa, a kuma zauna tare da iyali ko dangi ko abokai a cikin nishaɗi, a ƙalla mutane za su kasance cikin farin ciki kwana uku ajere, kafin a fara komawa cikin aiyukkan yau da kullum a bar yara da mata suna nuna kwalliya da ziyarce-ziyarce.A wurin jami’an tsaro dake kan iyakokin Nijeriya lamarin kam ya saɓa domin ba dukkan lamurran da suka shafi sallah suke samu ba.Wani jami’in kula da kayan da ake shigo da su a ƙasa(custom) a garin Kamba ya ce suna yin sallah ne cikin godiyar Allah amma ba za ka haɗa da wanda yake cikin iyalai da dangi ba.”Mu anan sallar Idi ƙarama ko babba ba ta da bambanci da sallar juma’a a wurinmu domin halayyar Hausawa da ake yi na rabon abinci a ƙwabta nan an ɗauke mu ma’ikata baƙi ba a kawo mana, ranar Sallah ka samu mutum na dafa abinci da kansa don ba in da zai je ya saya.”Ya ƙara da cewar wasu lokutan mutanen gari da ake hulɗar arziki da su ana samu su kawo abinci ga ma’aikata amma saboda yanayin aiki da tsaro ba a karɓa, mutum matuƙar ba iyalinsa ko wurin sayar da abinci ba da wahala mutum ya ci abincin wani gida haka na ƙara sanya a lokacin sallah ma’aikata na wahala a gefen abinci.Shi ma wani ma’aikacin ya ce suna shan wahala a lokacin sallah saboda ƙarancin abinci, wannan ba komai ba ne yanayin aiki ne ya zo da hakan domin ba za ka ci abincin da wani mutumin gari ya dafa, in da ake samun sauƙi akwai ma’aikata ‘yan uwa da sukan zo da matansu a wurin aiki su ne za su aiko wa takwarorinsu abinci ba don haka ba sai wahalar ta ƙaru sama da wadda ake ciki.Ya ce mafiyawan waɗanda ke aiki bakin boda a lokacin sallah sukan shiga damuwar kaɗaici sai dai ba yanda suka iya aiki ne na sadaukarwa shi kuma irin haka dole ta same ka.






