ZEZA’S CUISINE
Hadin Lemun Manguro da Abarba
Abubuwan bukata
Mongoro
Abarba
Sugar
Ruwa
Yadda ake hadawa
Da farko za ki bare mongoro da Abarba ki yanka sannan ki sa sugar sai ki sa shi a blender sai ki sa ruwa ki yi blending nashi saiki tace in kina son flavor sai ki sa, sai sa a fridge shikenan.
Akwai bukatar sanya natsuwa a wurin hadawar domin ki yi abinki daidai gwargwado yanda zai yi dadi da dandano, kar ki sanya kayan su wuce bukatar ku, ki yi yanda za a samu daidaito a tsakani.
Duk macen da ke yin wannan hadin a gida za ta hutar da maigidanta ga sayen lemun kwalba ko na kwali ko kwalba, domin wannan hadin na musamman ne da bai da wani sinadarin hana lalacewar abu, wanda shi kansa wasu masana na fadin yana da tashi illa.
Mata mu rika shayar da mzajenmu abin sha daga kayan marmari kai tsaye ba tare da an sanya masu wasu sinadarai ba, don kara inganta lafiyarmu da ta iyalanmu.
ENJOY
By:Zainab Muhammad jibril
(Zeza’s cuisine).





