PDP ta sake samun koma baya kan rikicin shugabanci da ya mamaye ta
PDP ta sake samun koma baya kan rikicin shugabanci da ya mamaye ta
Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya ce shugabannin jam’iya na yanzu ba za su iya kai jam’iyar ga nasara ba a 2023 ba, akwai bukatar sauke su.
Wike tare da wadanda suka aminta da ra’ayin a cire shugaban PDP Uche Secondus hakan ya haifar da tsagewar PDP.
Gwamnoni da sauran jagororin PDP sun rabu gida biyu kan makomar shugabansu sai dai an cimma matsayar gudanar da babban taron a watan Okotoban wannan shekara domin kawai magance rikicin da ya dabaibayi PDP aka jawo taron baya maimakon watan Disamba.
Shugabannin gudanarwar jam'iyar NWC sun kasa aiwatar da abin da aka umarce su da gudanarwa na kiran taro a Talatar da suka sanar a farko.
A ranar Talata Wike ya ce matukar PDP ba ta cire Secondus ba tau bata son nasara a 2023, mutanen Nijeriya na son PDP ta karbi mulki amma ita ba da gaske take ba.
Ya ce da wadan nan shugabanni da wuya PDP ta samu nasara kan jam'iya mai mulki ta APC domin gazawarsu ta bayyana.
managarciya