Home Siyasa Obi ya hango zai mutu kafin zaɓen 2027

Obi ya hango zai mutu kafin zaɓen 2027

27
0

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa akwai yiwuwar ba zai rayu har zuwa zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 ba.

Obi ya yi wannan furuci ne yayin wata hira da aka wallafa a shafin X na mai gabatar da shirye-shirye, Chude Jideonwo, inda ya zargi gwamnatin tarayya da hana shi gudanar da harkokinsa tare da matsa lamba kan ‘yan adawa.

Ya ce yana fuskantar cikas a kusan dukkan abubuwan da yake yi, yana mai zargin cewa gwamnati na taka rawa wajen hana shi wasu hakkokinsa, duk da cewa bai gabatar da hujjojin da ke tabbatar da zarge-zargen ba.

Obi ya kuma ce ya taɓa fuskantar matsala a wani filin jirgin sama inda aka kulle motarsa, yayin da ya ƙara da cewa wasu mutane na guje wa gaishe shi a bainar jama’a saboda tsoron abin da ka iya biyo baya.

Har ila yau, ya yi zargin cewa wasu daga cikin magoya bayansa kan roƙe shi kada ya halarci bukukuwan iyalansu saboda tsoron abin da hakan ka iya jawo musu.

Zuwa lokacin wallafa rahoton, gwamnatin tarayya ba ta mayar da martani kan zarge-zargen da Obi ya yi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here