Home Siyasa Obasanjo ne ya haɗa Obi da Kwankwaso domin zaɓen 2027 – tsohon...

Obasanjo ne ya haɗa Obi da Kwankwaso domin zaɓen 2027 – tsohon mai ba shi shawara

27
0

Obasanjo ne ya haɗa Obi da Kwankwaso domin zaɓen 2027 – tsohon mai ba shi shawara

Tsohon mai ba tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, shawara kan harkokin siyasa, Akin Osuntokun, ya bayyana cewa Obasanjo ne ya taka muhimmiyar rawa wajen haɗa Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso domin ƙulla ƙawancen takarar shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027.

Osuntokun ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar ARISE News, inda ya musanta zargin cewa Obasanjo na goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Ya ce idan har za a ce Obasanjo na mara wa wata tikitin takara baya, to ita ce tikitin Obi da Kwankwaso, yana mai cewa tsohon shugaban ƙasar shi ne babban jagoran ƙoƙarin haɗa su.

A cewarsa, babu hujjar da ke nuna cewa Obasanjo na aiki a ɓoye domin Tinubu, yana mai cewa dukkan abin da yake yi a siyasance ya nuna inda goyon bayansa yake.

Osuntokun ya ce Obasanjo ne ya shirya ganawar Obi da Kwankwaso tare da sauƙaƙa tattaunawar da ta kai ga ƙulla ƙawancen, yana mai cewa dukkansu suna da kyakkyawar alaƙa da tsohon shugaban ƙasar.

Ya ƙara da cewa wannan tikitin na da ƙarfi kuma zai iya yin tasiri sosai a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Tsohon mai ba Obasanjo shawarar ya kuma bayyana cewa tun kafin zaɓen 2023 an yi yunƙurin haɗa Obi da Kwankwaso, yana mai cewa da sun cimma matsaya a lokacin, da sun iya cimma yarjejeniyar raba wa’adin mulki tsakaninsu.

Osuntokun ya kuma ce haɗin Obi da Kwankwaso ya fi tikitin da Jam’iyyar Labour ta fito da shi a zaɓen 2023 ƙarfi da kuma jan hankali, yana mai bayyana shi a matsayin tikitin da ya fi dacewa da yanayin siyasar Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here