Na san talakawan Nijeriya na shan wahalar cire tallafin mai - Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce ya fahimci irin wahalhalun da ke tattare da cire tallafin man fetur, yana mai tabbatar da cewa matakin na da amfani ga kasar nan, musamman wajen tabbatar da ci gaba a nan gaba.
Tinubu, wanda ya karbi bakuncin tsoffin gwamnoni 18 da su ka yi gwamna tare a 1999, a fadar shugaban kasa, ya roki ƴan Najeriya da su kara hakuri.
Ya kuma tabbatar wa ƴan ƙasa cewa ana shirin aiwatar da tsarin da zai magance radadin cire tallafin man fetur.
Tinubu ya ce gwamnati za ta kara kokari, ta hanzarta aiwatar da samar da tallafi ga ƴan ƙasa, musamman tallafin kuɗaɗe, inda ya tabbatar da cewa za a raba tallafi ba tare da almundahana ba.
"Na fahimci cewa mutanenmu suna shan wahala. Kowa ya san ba za a iya haihuwa ba tare da ciwo ba. Murnar haihuwa shine jin daɗin da ke zuwa bayan ciwo. Najeriya ta riga ta sake haihuwa ta hanyar cire tallafin mai. Wani mataki ne da ƴan ƙasa mafi rinjaye za su amfana a kan wasu tsirari. Don Allah a gaya wa mutane su ɗan yi haƙuri.”
"Jin dadi da sauki na nan zuwa. Ba na son raba tallafin na kuɗi ya fada hannun ƴan sama da fadi. Na san matakin akwai radadi. A karshe, za mu yi murna da ci gaban kasarmu,’’ kamar yadda ya shaida wa gwamnonin, wadanda tsohon Gwamnan Jihar Edo, Lucky Igbinedion ya jagoranta.
Daily Trust ta rawaito cewa tun da fari, Tinubu ya rubutawa majalisar wakilai cewa ya nemi a gyara kudurin kasafin kudi na 2023 domin fitar da Naira biliyan 500 don samar da ababen more rayuwa ga ƴan Najeriya.
managarciya