Home Siyasa Mun yi wa Tinubu gargaɗi kan matsalar tattalin arziki da tsaro amma...

Mun yi wa Tinubu gargaɗi kan matsalar tattalin arziki da tsaro amma ya toshe kunnuwan sa – Limaman mabiya Katolika

23
0

Tsohon Archbishop na Cocin Katolika a Abuja, John Onaiyekan, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai amince da ra’ayin da Kungiyar Limaman Katolika ta Najeriya (CBCN) ta gabatar masa ba game da halin da tattalin arziki, tsaro da siyasar ƙasar ke ciki.

Onaiyekan ya ce a ganawarsu da shugaban ƙasa a fadar shugaban ƙasa ranar 28 ga Yuli, limaman sun shaida masa cewa matsin tattalin arziki na ci gaba da jefa talakawa cikin wahala, amma Tinubu ya nace cewa gwamnatinsa na kan hanya madaidaiciya kuma tattalin arzikin ƙasar na inganta.

Ya bayyana cewa manufar limaman ba ta siyasa ba ce, illa cika nauyin da ya rataya a wuyansu na faɗar gaskiya kan matsalolin da ke addabar al’umma.

Har ila yau, Onaiyekan ya nuna damuwa kan yiwuwar Najeriya ta koma ƙasar da jam’iyya ɗaya ke mamaye siyasa, yana mai cewa dimokuraɗiyya na buƙatar sahihin zaɓe da kuma hukumar zaɓe mai zaman kanta. Ya buƙaci a yi garambawul ga tsarin naɗin shugabannin INEC domin ƙara amincewar jama’a.

Malamin ya kuma yi kira ga Shugaba Tinubu da ya fi mayar da hankali wajen magance matsalolin da ke addabar ‘yan Najeriya tare da kare cibiyoyin dimokuraɗiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here