Home Siyasa Mi ya sa ba a ga sunan Sheikh Jingir da Rarara ...

Mi ya sa ba a ga sunan Sheikh Jingir da Rarara a kwamitin yakin neman zaben Tinubu ba?

25
0

Mi ya sa ba a ga sunan Sheikh Jingir da Rarara ba a kwamitin yakin neman zaben Tinubu ba?

Jam’iyyar APC ta nada Sheikh Halliru Maraya daga Kaduna da Sheikh Aminu Abu Ammar a matsayin wasu daga cikin malaman da za su tallata takarar Tinubu a tskanain Musulmai a kwamitin yakin neman zaben Tinubu, yayin da a bangaren ‘yan fim aka samu Ali Nuhu da Mansurah Isah a matsayin wadanda za su tallata Tinubu a kwamitin.

Sai dai rashin ganin babban malamin Islama Sheikh Jingir wanda ya yi suna wajen tallata takarar Tinubu ta Muslim-Muslim a jerin malaman Islama da za su tallata Tinubu da fitaccen mawakin APC Rarara a cikin kwamitin yakin enman zaben Tinubu ya haifar da muhawara, inda wasu ke mamakin rashin ganin sunayensu yayin da wasu ke cewa za a iya sanya su daga baya ko kuma aikinsu bai zama dole sai an sanya su a cikin kwamitin ba. Ya kuke kallon wannan lamarin?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here