Matashi Ya dabawa abokinsa wuka ya mutu kan naira 50 a Sokoto
Matashi Ya dabawa abokinsa wuka ya mutu kan naira 50 a Sokoto
Matasa guda biyu fada ya kaure a tsakaninsu a lokacin da suke tsaka da yin wasan Kati wadda ake zaton caca ce suke yi, kan dayan ya cinye naira 50, dayan bai aminta da cinyewar ba ya yi ikirarin dabawa abokinsa wuka matukar bai ba shi naira 50 din ba, haka aka yi kuwa ya soka masa wuka a ciki abin da ya yi sanadin barinsa duniya.
Majiyar da ta tabbatar da faruwar lamarin ta shedawa manema labarai cewa a Unguwar Assada cikin karamar hukumar Sakwato ta Arewa a jihar Sakkwato matashi Yasir Hassan mai shekara 15 ya dabawa abokinsa Mutaka Bello mai shekara 19 wuka a ciki bayan gardama ta kaure a tsakaninsu domin Yasir ya samu nasarar cinye naira 50 a wasan da suka buga ta kati(WHOT) amma Mutaka ya ki bayar da kudin.
Kamar yadda majiyar ta ruwaito, "Yasir ya yi ikirarin Kashe Muttaka in bai bayar da kudin naira 50 ba, yayin da Muttaka ya hana kuma ya ce "Zo gani ka kashe ni, nan take Yasir ya zaro wuka daga jikinsa ya dabawa Muttaka a ciki, sauran yaran dake a harabar Furamaren Magajin Gari suka watse kowa ya yi ta kansa, bayan an sanar da iyayen Muttaka halin da yake ne suka zo suka duke shi zuwa assibiti sai dai tun kan hanya rai yayi halinsa." a cewarsa.
A lokacin da wakilinmu ya tuntubi jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Sakkwato ASP Sanusi Abubakar kan lamarin ya ce yanzu baya cikin birnin jiha sun je karamar hukumar Sabon Birni amma zai yi masa magana daga baya.
Har zuwa hada rahoton bai waiwayi wakilinmu ba kan wannan lamarin da bai yi wa mutane dadi ba.
managarciya