Home Manyan Labaru Matar Gwamnan Kano, ta shigar da ƙarar neman saki a kotun...

Matar Gwamnan Kano, ta shigar da ƙarar neman saki a kotun Abuja

41
0

Zainab Musa Kwankwaso, matar gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ta shigar da ƙarar neman raba aurensu a wata kotu da ke Gudu, Abuja.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa takardun kotu sun nuna cewa Zainab, wadda ’yar tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ce, ta nemi a raba auren bisa tsarin Khul’i, wanda mata ke amfani da shi wajen neman saki a Musulunci, ta hanyar mayar da sadakin da aka biya.

Takardar sammacin mai lamba CV/97/26 ta umarci gwamnan da ya gurfana a gaban kotun ranar 17 ga watan Nuwamba, 2026.

Zainab ta auri Abba Kabir Yusuf a ranar 29 ga Yuli, 2006, lokacin da ta ke aiki a matsayin hadimar mahaifinta, inda su ka haifi ya’ya shida tare.

DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa a cikin bayanan ƙarar, Zainab ta ce aurensu ya shiga mawuyacin hali sakamakon rashin kulawa, soyayya da kusanci tsakanin ta da mijin nata.

Ta bayyana cewa ita ma ta yanke ƙauna da sha’awar ci gaba da auren, har ta kai ga samun tsananin ƙyamar zamantakewar auren.

Ta kuma bayyana fargabar cewa ci gaba da zaman auren zai iya jefa ta cikin halin rashin iya kiyaye dokokin Allah da suka shafi wajibcin mace ga mijinta.

DAILY NIGERIAN ta kuma rawaito cewa a takardun kotun, Zainab ta ce duk ƙoƙarin da aka yi na sasanta tsakaninsu da dawo da zaman lafiya ya ci tura, tana mai zargin cewa ta fita daga zuciyar gwamnan a matsayin ta na mai ɗakin sa.

Saboda haka, a cewar rahoton, ta bayyana shirinta na mayar wa gwamnan sadakin da ya biya a lokacin aurensu domin samun damar raba auren.

Rahoton ya kuma bayyana cewa rikicin auren na zuwa ne bayan samun saɓani tsakanin gwamnan da ubangidansa na siyasa kuma surukinsa, Rabiu Musa Kwankwaso, kimanin shekara guda da ta gabata.

Majiyoyin jaridar sun ce tun ranar 28 ga Oktoba ne matar gwamnan ta bar gidan gwamnatin Kano zuwa gidan mahaifinta da ke Miller Road, Kano, kafin daga bisani ta tashi zuwa Abuja ba tare da rakiyar jami’in ’yansanda da aka ba ta ko sauran jami’an tsaro ba.

Rahoton ya yi zargin cewa lamarin ya jawo kamen wasu jami’an tsaro da ke gadin ɓangaren da take zaune a gidan gwamnati da kuma waɗanda ke aikin tsaro a gidan Kwankwaso, kafin daga bisani aka sake su bayan yi musu tambayoyi.

Haka kuma, rahoton ya ce ’yansanda sun gayyaci babbar ’yar’uwarta da babban ɗan uwanta, Ado Kwankwaso, domin yi musu tambayoyi kan zargin taimaka mata wajen barin Kano.

Sai dai an bayyana cewa akwai zargin ana matsin lamba ga ’yan sanda domin gurfanar da Ado kan zargin satar mutum.

A wani ɓangare kuma, Kwamishinan yaɗa labarai na Kano, Sanusi Dawakin Tofa, bai mayar da martani ga kiran waya da saƙon da jaridar ta aika masa domin jin ta bakin gwamnan kan batun ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here