Ɗan takarar gwamnan Jihar Kebbi na jam’iyyar ADC, Abubakar Malami, ya yi kira da a dawo da tallafin man fetur domin rage radadin tsadar rayuwa da matsin tattalin arzikin da jama’a ke fuskanta a Arewa maso Yamma.
Malami ya ce cire tallafin ya ƙara tsadar rayuwa, tare da jefa iyalai cikin mawuyacin hali na tattalin arziki, musamman a yankin Arewa maso Yamma.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja, yayin da yake rattaba hannu kan yarjejeniyar Northwest ADC Governorship Candidates’ Compact 2027–2031, tare da sauran ’yan takarar gwamna na jam’iyyar ADC daga jihohin yankin.
A cewarsa, dawo da tallafin man fetur na daga cikin matakan gaggawa da ya kamata gwamnati ta ɗauka domin rage wahalhalun tattalin arziki da al’umma ke fuskanta.






