‘Yan bindiga sun kashe mutane bakwai tare da yin garkuwa da wasu da ba a tantance adadinsu ba a ƙaramar hukumar Ƙaura-Namoda dake Jihar Zamfara.
Maharan sun afka garin ne da misalin karfe 1:00pm na daren Juma’a, inda suka kai hari a unguwannin Tsohuwar Kasuwa, Matoya da Tsohuwar Tasha.
A cewar shaidun gani da ido, maharan sun rarraba kansu gida-gida domin raba hankalin jami’an tsaro a lokacin da suke kokarin kawo dauki.
Mutane biyar daga cikin wadanda suka mutu ‘yan sa-kai ne masu aikin tsaron gari, yayin da biyu kuma fararen hula ne ‘yan garin.
Zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a tantance adadin wadanda aka yi garkuwa da su ba, kuma hukumomin tsaro ba su yi magana a kai ba.
Dakta Ayuba Muhammad Ƙaura ya yi ƙarin bayani ya ce abin da ya faru ‘yan bindiga sun kashe mutane bakwai sun raunana wasu daga cikin waɗanda suka ji rauni yanzu haka suna asibiti, “ina jin harbi ina cikin gidana a lokacin da suka shigo har an ji suna cewa tunda sun gama da masu tsaron gari gobe ma za su dawo ka ga kenan ana tsammanin dawowarsu anan tsakiyar garin Ƙaura.
“Mata ne suka tafi da su domin maza da yawa ba su kwana a gidajensu har yanzu ba a san adadin mutanen da suka yi garkuwa da su ba.”
DSP Yazid Abubakar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Zamfara ba ya kusa ga waya a lokacin da waƙilinmu ya kira shi don samun ƙarin bayani.






