Wani lauya ya yi ƙarar mawaƙan nan Dauda Kahutu Rarara da Adamu Fasaha a Babbar Kotun Jihar Kano kan zargin ɓata sunan Farfesa Isa Ali Pantami, tare da neman su biya diyya ta ₦100 biliyan.
Arewa Updates ta rawaito cewa, yayin shigar da ƙarar, lauyan, Sirajo Abubakar, ya buƙaci kotu ta bayyana cewa waƙoƙin da su Rarara suka yi sun taɓa ƙima da martabar Pantami.
Takardar ƙarar ta bayyana cewa ana zargin Rarara da Adamu Fasaha da wallafa waƙoƙi da bidiyoyi da suka jingina wa Pantami zarge-zargen da suka haɗa da shan miyagun ƙwayoyi, maye, sata da mallakar dukiyoyi da aka samu ta hanyar cin hanci da rashawa.
Haka kuma mai ƙarar ya buƙaci kotu ta hana waɗanda ake ƙara ci gaba da wallafa irin waɗannan waƙoƙi, tare da umartar su su janye waɗanda suka wallafa da ake ƙorafi a kansu da kuma neman afuwar Pantami a manyan jaridu biyar da shafukansu na sada zumunta.






