Home Siyasa Kotu ta tura Shugaban Matasan ADC Gidan Yari a Kebbi

Kotu ta tura Shugaban Matasan ADC Gidan Yari a Kebbi

12
0

Jami’a ln tsaro sun kama shugaban matasan jam’iyyar ADC na jihar Kebbi, Hon. Muhammad Al’amin, tare da tura shi gidan gyaran hali.

Rahoton ya ce a safiyar yau Alhamis ne aka gayyaci Muhammad domin amsa tambayoyi kafin daga bisani aka gurfanar da shi a gaban Kotu, inda daga nan ne aka tura shi gidan yari.

Anzargi shugaban matasan ne da furta wasu kalaman tada hankali da tunzura jama’a.

Sai dai makusantansa sun musanta hakan tare da alakanta kamashi da yunkurin hana ‘yan adawa motsi a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here