Home Labarai Kotu ta ba da umarnin rataye wasu mutum uku a Sakkwato

Kotu ta ba da umarnin rataye wasu mutum uku a Sakkwato

10
0

Babbar kotun jihar Sakkwato ta yanke hukuncin kisa ta hanyar ratayewa ga wasu mutum uku ciki har da wani ɗan ƙasar  Nijar ɗaya, saboda  kama su da laifin ta’addanci da safarar miyagun makamai da ta yi.

Waɗanda aka zarta wa hukuncin akwai Yusuf Muhammad wanda aka fi sani da Sallau, ɗan Nijar kenan da Jaɓɓi Alhaji Yalle da Kabiru Muhammad an zartar masu da hukuncin ne kan aikata manyan  laifukan da ke da haɗi da  ta’adanci da safarar miyagun makamai.

Hukumar kula da harkar tsaro ta farin kaya DSS ne suka kama mutanen a shekarar da ta gabata 13 June 2025, a wani bayanin sirri da suka samu a cikin aikin da suke yi na kawar da safarar miyagun makamai a iyakokin Nijeriya.

A ƙarar da aka shigar gaban Alƙali Muhammad Nuraddeen  Bello SS/45C/2026, a babbar kotun Sokoto mai namba 23 ne aka gudanar da shari’ar.

A lokacin da yake yanke hukunci Alƙali Bello ya ce  ƙarar lafiya lau take tana saman doka,  shigar da zargi kan waɗanda ake tuhuma in da aka yanke ma dukkan su ukun hukuncin kisa ta rataya.Kotu ta bayar da umarnin duk kuɗin da aka samu daga hannunsu a lokacin da ake bincike a hannun ta su ga gwamnatin tarayya.

Alƙali Bello ya bayyana hukuncin wani ɓangare ne na ƙoƙarin jami’an tsaro na ganin sun katse ɗaukar nauyin ta’addanci da kuma safarar miyagun makamai a iyakoki ciki da wajen Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here