Lauya A.M Jariri, Esq. ya ce Shima wannan ba Adalci bane!
A bayanin da ya wallafa a rurakarsa ta Facebook ya yi dogon bayani kan rashin dacewar korar mutanen a wurin da suke neman abinci da sunan wai za a gyara fasalin gari.
“Bayar da umarnin kwana ɗaya (awanni 24) ga masu sana’o’in kan hanya a gefen Asibitin UDUTH da Ma’aikatar Filaye da Gidaje ta Jihar Sokoto ta yi ba daidai bane kuma rashin adalci ne.
“Tabbas Gwamnati karkashin ma’aikatar filaye da gidaje na da ikon tsara hanyoyi, birane da kuma kawata su, amma dole ne ya kasance cikin adalci, mutunci, da bin ka’idojin shari’a.
“Tsarin birane bai kamata ya zama dalilin rusa rayuwar talakawa ko jefa su cikin tsananin wahala ba, musamman duba da cewa waďannan sana’o’i suna kusa da babban asibitin tarayya, inda marasa lafiya da masu jinyar su ke dogaro da su wajen biyan bukatun gaggawa. A sakamakon wannan umarnin, marasa lafiya zasu iya shiga wahalar da zata iya sanadin rasa rayuka da yawa.
“Muna kira ga Gwamnatin Jihar Sokoto karkashin Ma’aikatar Filaye da Gidaje, da ta ƙara wa’adin da aka bayar zuwa wani wa’adi mai ma’ana, domin bai wa waďannan bayin Allah damar kwashe kayan su cikin mutunci da kuma samun wani wuri na cigaba da sana’o’in su.
“Haka kuma, ya dace Gwamnati ta auna sauki da ribar da waďannan sana’o’i ke kawowa marasa lafiya talakawa da masu jinyar su, musamman a lokutan gaggawa da ake bukatar abinci ko wasu muhimman kayayyaki.”




