Home Labarai Karɓe Kadarori: Malami Ya Ƙalubalanci EFCC a Kotu

Karɓe Kadarori: Malami Ya Ƙalubalanci EFCC a Kotu

6
0

Tsohon Antoni Janar na Tarayyar Najeriya (AGF), Abubakar Malami, ya shigar da ƙara a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja, yana ƙalubalantar umarnin rikon wucin-gadi (interim forfeiture) na wasu kadarorinsa da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ƙwace.

A ranar 6 ga Janairu, Mai shari’a Emeka Nwite na Kotun Tarayya da ke Abuja ya bayar da umarnin rikon wucin-gadi na kadarori 57, waɗanda EFCC ke zargin an samo su ne ta hanyoyin da ba su dace da doka ba.

Malami, ta hannun lauyoyinsa, ya roƙi kotun da ta soke wannan umarni, yana mai jaddada cewa ba a ba shi damar kare kansa yadda ya kamata ba kafin a yanke hukuncin rikon kadarorin.

Haka kuma, ya nemi kotun da ta hana EFCC ci gaba da ɗaukar wani mataki a kan kadarorin har sai an kammala sauraron ƙarar da ya shigar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here