Home Labarai Kai ya rabu kan aiyukkan Hisbah a jihar Sokoto

Kai ya rabu kan aiyukkan Hisbah a jihar Sokoto

35
0

Gwamnatin jihar Sakkwato ta sake dawo da aiyukkan Hisbah shekarru biyu da suka wuce bayan dakatar da aiyukkanta da Gwamnatin da ta gabata ta yi saboda zargin wuce gona da iri da cin zarafin mutane a jihar Sakkwato.

Bayan da gwamnatin Ahmad Aliyu ta sabunta dokar samar da hisba a jiha aka ƙaddamar da ita ta soma aiki a birnin jiha in da wasu ke sukar aikin wasu kuma suna sam barka da samar da hukumar domin taimakawa jami’an tsaro.

A kwanan nan hankalin mutane a wajen jiha ya karkato kan aikin ta a jiha in suka ƙaddamar da sintirin ‘Operations tsaftace gari’ in da suka yi nasarar kama mutane sama da 30 a unguwanni Ƙwannawa da Mabera da Damuwa da sauransu, sun samu kai samame a wasu manyan Otal kamar Pinacle da Duniya da wasu ƙanana da dama, abin da ya ƙara jefa masu laifi shiga cikin taitayinsu kan wuraren da suke zuwa aikata ɓarna.

Hukumar ta mayarda hankali wurin hana Karuwanci da shan giya da tu’amali da miyagun ƙwayoyi a birnin jihar, a wurin gudanar da aikin da yawan mutane na zargin hukumar da wuce gona da iri da saɓawa doka, abin da ke hana cimma burin da aka kafa su don shi.

Hisbah ta samu nasarar rufe Otal ɗaya a kan titin Kano, ta kuma kai samame a wasu wuraren da ake sayar da kayan maƙulashe kan tintin Maiduguri don tabbatar da ba aikata aikin baɗala a wurin, sun shiga harkokin gyaran aure da matsalolin iyali sama da 500 kamar yadda bincik ya nuna.

Muhammad Nasir wani mai sharhi ne kan al’amuran yau da kullum a jiha ya ce akwai buƙatar sake duba aiyukkan Hisbah a jiha domin suna ke ta haƙƙin masu laifi da suke kamawa, ba su mutunta masu laifi a lokacin da suke aiki, suna walaƙanta su wanda hakan bai dace ba, in mace ta zama Karuwa walaƙanta ta ba zai sa ta gyara halinta ba, musguna mai yin shaye-shaye ba zai sa ya bar halinsa ba, amma mutuntawa da ba da shawara zai sa mutum ya gyaru a cikin natsuwa, yakamata a gyara yanda ake tafiyar da hukumar don samun nasara.

Barista Sidi Bello lauya ne a jihar Sakkwato ya ce “dokar da ta samar da dokar Hisbah ta ci karo da dokar qasa, kasan yanzu Nijeriya ba biyayya ake yi wa doka ba, shugabanni ake biya, duk abin da shugaba ke so, ba dubin shi za a yi bisa muhalli ba, kan doka ta ba da damar yi ko akasin haka, abin da ake dubi kawai ra’ayin gwamna da abin da yake so, masu haqqin ba shi shawara kan doka ba su iyawa domin yaransa ne, kwamishinan shari’a shi ke da alhakin duk dokar da za a yi a jiha ta zama ba ta savawa dokokin tsarin mulki ba, kafin gwaman ya fara jan ragamar mulki sai ya yi rantsuwa zai kare manufofi da qudurorin tsarin mulki, ka ga kenan duk abin da zai yi yakamata ya duba abin da tsarin mulki ya aminta da shi, amma anan sai a rinqa yi kamar wata buqata muke son cimma ba Nijeriya ba.

“Wannan doka tun farko ba a kafa ta bisa ga doron kundin tsarin mulki ba, aiyukkan Hisaba na cikin aiyukkan da tsarrin mulki qarara ya haramta, kashi na uku qaramin kashi na xaya na tsarin mulki ya haramta kowane vangare na jiha ya aiyana kansa matsayin mai tafiya bisa ga doron wani addini,(is circular State) ita Hisba an xauko ta ne cikin musulunci, ba muslmi ne kaxai ke zave a Sakkwato ba, sannan sashe na xaya qaramin sashe ya ce kundin tsarin qasa na gaba ga kowane tsari, dokar qarara ta savawa qaramin kashi na xaya da uku ya buge ta duk wata doka da ta yi karo da tsarin mulki wannan haramtacciya ce.

“Yawon da suke yi zuwa Otal Otal suna kama mutane da sunan cewa suna alfasha wannan ko a shari’ar musulunci bai hallata ba, ba a ta Jassushi, tsarin mulki ya baiwa mutum haqqin sirrantawa, matuqar mutum ba fitowa ya yi a fili yana aikata laifi ba, in har kuna ganin Otal wuri ne da ake aikata laifi missa aka bari aka gina shi.

“Ka tun da gwamnatin siyasa ce ake haka, shi tsarin mulki ya baiwa musulmi dama ya bi addininsa yanda yakamata, kamar Aure, saki, gado, wasiyya, waqafi, shari’ar musulunci yakamata a wanzar a jiha, duk abin da a tsakaninmu yake kundin tsarin mulki ya ba mu damar aiwatar da shi. musulunci na kula da mutunci da irlin mutane, in dai mutum bai yi tallar laifi ba, ba a kama shi.

“Yakamata hukumar hisba su mayar da hankali kan yaran da ake kawowa karatun allo, ka ga malami da yara sama da 80 yana kula da su, da wanda haqqin kulawar ba hannunsa suke ba, har gwamnan Sakkwato ke qoqarin qarfafa lamarin ta hanyar fara baiwa makaraun tsangaya albashi, hakan nasa malami ya tafi ya samo yara domin albashin da za a riqa ba shi, kasan yaran nan ba karatu suke ba, suna yawon zuwa gidajen mutane ne wurin shara da wanke-wanke, da zama a tashoshin mota da gidajen mai da gidan Karuwai, su ne yakamata hukumar Hisba ta ilmantar saboda sun xauki abin da suke yi addini ne, don su san abin da suke yi ba addini ba ne matsala ce ga tarbiya, wasunsu ne ke iya zama ‘yan bindiga domin babu kula ta iyaye,”kalaman Barista Sidi.

Kwamadan Hisbah a jihar Malam Usman Jatau ya ce hukumar su tana aiki saman doka, kuma tana samun nasara kan aikace-aikacen ta, ba ta neman Soja Boy, Y Amerika ne kawai suke nema ruwa Jallo, “ba mu da issue da Soja Boy, Kano ke nemansa, mu dai wanda muke nema Y Amerika ne shi muke son mu kama kamar mi, mun kama ‘yan matansa biyu suna hannunmu.”

Kan yawan mutanen da suka kama ya ce su ba su riƙe mutane a hannusu ba su iya ba da yawan waɗanda suka kama, “muna da dokar kar a riƙe mutum sama da awa 78, sai in binciken mu bai ƙare ba ne suke kai hakan, in mun kammala bincike muna da wurare guda uku da muke hannuntawa masu laifi da suka ƙunshi Hedikwatar ‘yan sanda da ofishin ‘yan sanda da hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi in harkar ƙwaya ce don turawa zuwa gidan yari ta hanyar lauyanmu da amincewar kwamishinan Shari’a na jiha.”

Kan zargin wuce gona da iri da dukan masu laifi da shiga hurumin da shari’ar Musulunci da dokar ƙasa ba ta aminta ba da jami’an hisbah ke yi, ya ce “shi ne ban sani ba in da hurumin addini ya hana a shiga in ana ɓarna, dokar ƙasa ba ta ce mutum ya keɓe ya yi sharholiya ba, ni banga dokar Nijeriya da ta faɗi haka ba, amma ta faɗi mutum yana iya yin abin da yake so wanda bai saɓawa dokokin ƙasarsa ba, sai mu kalli in mutum musulmi ne dokokin ƙasa zai martaba ko dokokin Allah da Manzonsa, a haka muke bin dokokin ƙasa dana shari’a don mu ga an hana, ba wata Otal a Sakkwato da ba mu aikawa takardar ƙa’idojin da ake son su bi a wurin gudanar da wuraren su ba, cewa ba a shan giya ba a kai mata a wuraren domin yin mu’amalar banza, waɗannan sun saɓawa ɗabi’un mutanen Sakkwato, ya saɓawa addinin Allah da dokokin jiha da Nijeriya, muna yin aikin ne bisa ga doka ba ga kai ba.”

Malam Murtala Bello Ɗa’a malamin addini ne a jiha ya nuna gamsuwarsa ga aiyukkan na Hisbah amma ya ba da shawara a kai, “aiyukkan da suke yi na kame yakamata tun farko sun yi domin tubalai biyu ne aka gina aikin hisbah a kai waton yin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, abin da suka yi ya yi kyau zai tsaftace gari ya kawo cigaba da kawo zaman lafiya, ban ga suna wuce gona da iri ba amma wanda ya ga haka yakamata ya bayar da misali.

“Ni na gamsu da yanda suke aikin su a baya hisbah ba ta komai amma a yanzu suna ƙoƙari, abin da ya da ce su sanya a gaba biyu ne, mutane sun yi nisa a wurin tauye ma’auni duk in da ake awo na shinkafa, dankali, albasa, da sauransu yakamata su mayar da hankali a wurin, sannan su kuma mayarda hankali kan matasa da zaran sun ga an fara ta’addanci su ɗauki mataki yanda yakamata gwamnati ta gane cewa suna aikin al’umma ne bana siyasa ba.” 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here