Home Labarai ‘Yan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar APC a Kano

‘Yan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar APC a Kano

9
0

‘Yan bindiga sun kashe Alhaji Garba Buba, shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na Rantan Ward, a ƙaramar hukumar Bebeji ta jihar Kano.

Rahotanni sun ce wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka harbe shi har lahira. Har yanzu ba a samu cikakken bayani kan dalilin harin da kuma ko an kama wadanda ake zargin ba.

Lamarin ya sake jawo hankalin jama’a kan matsalar tsaro da ake fama da ita a wasu sassan jihar Kano.

Akwai buƙatar gwamnati ta tashi tsaye domin daƙile matsalar kar ta wuce hannun kowa a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here