Home Siyasa Hukumar Zaɓe za ta sanar da shirin ta kan zaɓen 2027 ga...

Hukumar Zaɓe za ta sanar da shirin ta kan zaɓen 2027 ga mutanen Nijeriya

14
0

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta shirya gudanar da taron masu ruwa da tsaki da kuma taron manema labarai a Abuja ranar Talata, 6 ga Oktoba, 2026, domin bikin cikar kwanaki 100 kafin babban zaɓen shekarar 2027.

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, zai gabatar da bayani kan shirye-shiryen da hukumar ta kammala da kuma waɗanda take ci gaba da yi gabanin babban zaɓen.

A cewar INEC, batutuwan da za a tattauna a taron sun haɗa da rajistar masu zaɓe, tantancewa da gabatar da sunayen ’yan takara, shirye-shiryen kayan aiki da ma’aikata, da kuma matakan da hukumar ke ɗauka domin tabbatar da sahihanci da amincin tsarin zaɓe.

Hukumar ta bayyana cewa taron na daga cikin matakan da take ɗauka domin tabbatar da gaskiya da bayyana muhimman bayanai ga jama’a a kan lokaci, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumar da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin zaɓe.

Ana sa ran shugabannin jam’iyyun siyasa, jami’an tsaro, ƙungiyoyin farar hula, masu sa ido kan zaɓe, jami’an diflomasiyya, shugabannin addinai da na gargajiya, ƙungiyoyin matasa, masu fafutukar kare haƙƙin mutanen da ke da nakasa, da kuma ’yan jarida za su halarci taron.

INEC ta kuma ce za a watsa taron kai tsaye ta wasu gidajen talabijin na ƙasa da kuma kafafen sada zumunta na hukumar.

Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara tunkarar babban zaɓen 2027, wanda ake sa ran zai kasance ɗaya daga cikin muhimman zaɓuka a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here