Home Siyasa Hadimar Gwamnan Kano ta bayyana goyon bayan ta ga Atiku

Hadimar Gwamnan Kano ta bayyana goyon bayan ta ga Atiku

12
0

Ma taimaka wa Gwamnan Jihar Kano kan Kafafen Sadarwa na Zamani, Mufeeda Rasheed Galadanci, ta bayyana goyon bayanta ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jamʼiyyar ADC Alhaji Atiku Abubakar a zaɓen 2027.

Arewa Updates ta rawaito cewa, Mufeeda ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar kan matsayarta game da zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

Mufeeda ta bayyana cewa zaɓin Atiku shawara ce ta kanta, bisa ra’ayinta da abubuwan da take fata ga makomar Najeriya.

Ta kuma jaddada cewa tana mutunta haƙƙin kowane ɗan ƙasa na yanke shawarar wanda zai zaɓa bayan samun isassun bayanai.

Tun a Alhamis ɗin nan, ita ma ɗaya daga cikin hadiman gwamnan Kanon kan kafafen sada zumunta wadda ke da kusanci da Mufeeda, wato Khadija Aminu Shareef wadda aka fi sani da Deeda ta bayyana cewa Atiku Abubakar za ta yi a zaɓen 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here