Home Uncategorized Gwamnonin Zamfara sun yi alƙawarin samar da tsaro da magance matsalar talauci 

Gwamnonin Zamfara sun yi alƙawarin samar da tsaro da magance matsalar talauci 

9
0

 

Gwamnonin Zamfara na fara hula su biyar sun amince za su yi aiki tare don ganin an shawo kan matsalar tsaro da tattalin arziki a jihar.A wani taro na sirri da suka yi a gidan gwamnatin Zamfara ranar Assabar tsohon Gwamnan Ahmad Sani Yariman Bakura ya ce “wannan tafiya ina tabbatar maku abubuwa guda biyu za su bar tarihi a Zamfara na Farko matsalar tsaro da duk duniya na kallon Zamfara da ita, na biyu talaucin da ke akwai.

“Bayan matsalar tsaro za a ba da tallafi a tsakanin matasa maza da mata,” a cewarsa.Ya ce “za mu yi tawaga mai ƙarfi da za ta shafi mu biyar da sarakunanmu domin mu yi maganar da shugaban ƙasa kan matsalar tsaronmu, muna son goyon baya domin harkar tsaro ta jama’a ce gaba ɗaya ba ta mutum guda ba ce.”

Ya bayyana cewar sun yi alƙawarin magance waɗannan abubuwan guda biyu a jihar Zamfara ganin su ne ginshiƙan abubuwan da ke addabar jihar.
A bayanin da mai magana da yawun Gwamna Suleiman Bala Usman ya fitar kan taron ya ce masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC a Zamfara sun bayyana cikakken goyon bayansu ga sake zaɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamna Dauda Lawal a babban zaɓen dake tafe a shekarar 2027.
Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta gudanar da wani babban taron masu ruwa da tsaki a ranar Assabae a Fadar Gwamnati da ke Gusau.
Taron ya haɗa manyan jagororin jam’iyya, ciki har da tsofaffin gwamnonin jihar guda huɗu, zaɓaɓɓun jami’ai, dattawa, wakilan matasa da mata, tare da sauran masu ruwa da tsaki daga dukkan ƙananan hukumomi goma sha huɗu (14) na jihar.
A jawabin sa, Gwamna Lawal ya bayyana cewa taron ya zo a daidai lokacin da ake shirin fara harkokin siyasa gabanin zaɓen gama gari na 2027.
Ya ce, “Ya ku manyan masu ruwa da tsaki, shigarmu cikin APC ba kawai siyasa ba ce, illa wata dabara ce domin tallafa wa sake farfaɗo da Zamfara. Wannan ya ba mu damar aiki tare da Gwamnatin Tarayya, cin gajiyar shirye-shiryen ƙasa, da kuma bayar da gudunmawa ga cigaban jihar mu.
“Ina miƙa godiyata ta musamman gare ku duka bisa tsayayyen goyon bayan da kuka ba mu tun daga lokacin tuntuba, zuwa lokacin sauyin jam’iyya, har zuwa shigarmu APC. Wannan jajircewa taku ta taka muhimmiyar rawa wajen tsara wannan tafiya.
“Ya ku shugabanni da masu ruwa da tsaki, duk da cewa mun fito daga mabambantan akidu da muradun siyasa, aikin ceto da muke jagoranta nauyi ne na kowane ɗan jihar. Ba mallakin wata ƙungiya ko ɓangare ba ne. Wajibi ne na dawo da darajar jihar mu, sake gina cibiyoyi, tabbatar da tsaro, da samar da gwamnati mai aiki domin al’umma.
“A matsayinmu na masu ruwa da tsaki, gwamnati na mayar da hankali wajen dawo da daidaito, sake gina cibiyoyi, da samar da ci gaba a Zamfara. A cikin ɗan lokaci kaɗan, mun samu gagarumin ci gaba ta hanyar haɗin kai, shugabanci mai tsari, da jajircewar kowa.”
Gwamna Lawal ya kuma jaddada cewa komawarsa APC shawara ce mai zurfi da aka yi domin ƙarfafa shugabanci, inganta haɗin gwiwa tsakanin jiha da tarayya, faɗaɗa damar ci gaba, da kuma hanzarta isar da ayyuka ga al’umma.
“Wannan sabon mataki na tattare da ƙarin nauyi.

Dole ne mu tafiyar da buri da muradun siyasa cikin hikima, adalci, da tsari.
“Siyasa dabi’arta ta ƙunshi tattaunawa, sassauci, da samar da daidaito. Yayin da fagen siyasa ke faɗaɗa, haka kuma muradun mutane ke ƙaruwa. Yana da muhimmanci mu gane cewa ba dukkan buri ba ne za a iya cika su nan take.
“Jagoranci ba ya takaita ga mukamai kawai. Darajar siyasa tana fitowa ne daga hidima, tasiri, da bayar da gudunmawa ga ci gaban jihar.
“Ina tabbatar muku cewa adalci, daidaito, da gaskiya za su ci gaba da jagorantar dukkan shawarwarinmu. Za mu tabbatar da dimokuraɗiyyar cikin gida, bin doka da tsari, da kuma gaskiya a dukkan hulɗarmu. Aminci ga jam’iyya ya kamata ya tafi tare da ladabi.

Dole ne mu guji duk wani abu ko furuci da zai haifar da rarrabuwar kai ko raunana haɗin kanmu.”
A yayin taron, tsofaffin gwamnonin jihar, Ahmed Sani Yarima, Mahmuda Aliyu Shinkafi, Abdul’aziz Yari, da Bello Mohammed Matawalle sun bayyana cikakken goyon bayansu ga jam’iyyar APC tare da nuna goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Tinubu da Gwamna Lawal.
A cikin sanarwar da aka fitar, wacce Ministan Tsaro na Ƙasa (Ƙarami), Bello Mohammed Matawalle ya karanta, an bayyana cewa taron ya ba da damar tattaunawa mai zurfi kan haɗin kan jam’iyya, daidaita shugabanci, batutuwan tsaro, da shirye-shiryen manyan tarurrukan jam’iyya da zaɓen 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here