Home Rahoto Gwamnatin Sakkwato ta bayar da tallafin Miliyan 45 ga iyalan Margaya

Gwamnatin Sakkwato ta bayar da tallafin Miliyan 45 ga iyalan Margaya

13
0

Mataimakin gwamnan Sakkwato Alhaji Idis Mohammad Gobir ya yi kira da a riƙa bayar da rahoton duk wani abu da ba a yarda da shi ba ga jami’an tsaro domin ɗaukar matakin da yakamata..Mataimakin Gwaamna a lokacin da yake yiwa ‘yan gudun hijirar da suka gudu bayan kai hari da ‘yan bindiga suka yi a ƙauyen Ɗangulbi cikin ƙaramar hukumar Tureta in da suka kashe mutane 37 a sawu biyu da suka yi cikin kwana uku satin da ya gabata a jawabin jajantawarsa.Alhaaji Idris Gobir ya ce jami’an tsaro su kadai ba su iya yakar ‘yan bindiga a samu nasara ba da hadin kai da goyon bayan mutane ba.  “Nauyin da ya rataya kan kowace gwamnati na kan gaba shi ne kare rayukka da dukiyoyin ‘yan ƙasa, kan haka gwamnatin Ahmad Aliyu take kan gaba a yunƙurin kawar da ‘yan bindiga da ɓatagari a jiha.”Gobir ya jajantawa mutanen ya roƙi Allah ya gafatawa margayan daga nan ya ba da sanarwar taimako na miliyan 30 da buhun shinkafa 300 ga iyalan waɗanda aka kashe.Haka kuma gwamnati ta ba da tallafin buhun shinkafa 1,200 da miliyan 10 ga ‘yan gudun hijirar da ke yankin, sai miliyan biyar ga majinyatan da suka samu rauni a lokacin harin, mataimakin gwamna ya roƙi kwamitin da aka kafa domin raba tallafin ya yi adalci wurin rabon.Da farko muƙadashin shugaban ƙaramar hukumar Tureta Alhaji Umar ya godewa gwamnati kan kulawa da tallafin da ta baiwa waɗanda lamarin ya shafa.Waƙilin uban ƙasar Tureta Malam Bashir Sani ya nuna faricinkinsa ga gwamnati saboda ziyarar jaje da aka kawo masu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here