Gwamnatin Jihar Sokoto ta ayyana Jumu’a 24 ga Yuli 2026 a matsayin ranar hutu don bai wa ma’aikatan jihar damar yin rijista da kuma karɓar katin zaɓe.
Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan, Abubakar Bawa, ya fitar.
Ya ce Gwamna Ahmed Aliyu, ya buƙaci ma’aikatan jihar da su yi amfani da hutun domin yin rijista da kuma karɓar katin zaɓensu.
Sanarwar ta ce, gwamnatin ta kuma yi kira ga sauran al’ummar jihar da ba su yi rijistar ba da su yi amfani da ƙarin wa’adin makonni biyu da aka bayar domin yin rijista da karɓar katin zaɓen.






