Home Rahoto Gwamnatin Neja za ta bincike dalilin mutuwar matasa 37 hannun civil defense

Gwamnatin Neja za ta bincike dalilin mutuwar matasa 37 hannun civil defense

19
0

Gwamnatin Jihar Neja ta kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin mutuwar mutane 37 da suka rasu a hannun Hukumar Tsaro ta Civil Defence bayan kama su bisa zargin haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar Neja, Bologi Ibrahim, ya fitar a ranar Alhamis, 17 ga Satumba, 2026.

Lamarin ya biyo bayan samamen da NSCDC ta ce ta gudanar a ranakun Talata da Laraba, 15 da 16 ga Satumba, 2026, a yankin M.I. Wushishi/Lukoto, inda ta kama mutanen da take zargi da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

Daya daga cikin waɗanda aka kama Dauda Shehu, ya shaida wa Tashar Tsalle Daya cewa mutane 66 aka kama bayan ƙarfe 3:00 na ranar Laraba.

Ya yi zargin cewa wurin da aka tsare su ya yi tsananin zafi kuma babu isasshiyar iska, inda suka riƙa buga ƙofa suna sanar da jami’an cewa wasu daga cikinsu suna mutuwa, amma ya ce ba a saurare su ba.

Dauda ya ce tsananin halin da suka shiga ya kai ga wasu suna shan fitsarinsu, yayin da shi da wasu suka tsira saboda suna kusa da ƙofa inda suke samun iska kaɗan.

Malam Abdullahi, mahaifin ɗaya daga cikin waɗanda suka rasu, Salim Abdullahi, ya ce sun kai wa ɗansa abinci a ranar Laraba yana cikin ƙoshin lafiya, amma da suka koma ofishin NSCDC domin kai masa abinci a Alhamis sai suka tarar ya rasu.

Ya ce ya ga gawarwakin mutane sama da 30 a wurin.

Shi ma Malam Babawo Tudun Na Tsira kuma ya ce ƙaninsa mai shekara 17 yana cikin waɗanda suka rasu bayan kama shi a wurin haƙar ma’adanai.

Sai dai NSCDC ta ce tana zargin yiwuwar ɓarkewar wata cuta ce ta haddasa mutuwar, inda ta kai gawarwakin Babban Asibitin Minna domin gudanar da binciken lafiya don gano ainihin musabbabin mutuwar.

A jawabin da Gwamnan jihar Umar Bago ya gabatar ya ce, waɗanda suka rasu an ga alamar jikinsu yana saɓa ko ƙuna, wasu na fitar da kumfa da jini a bakinsu, inda ake zargin wata ƙila akwai wasu sinadarai a wurin da suke haƙar maʼadanan.

Kan hakan ne Gwamnatin Jihar Neja ta kafa kwamiti wanda Mataimakin Gwamna, Comrade Yakubu Garba, zai jagoranta, yayin da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Maurice Magaji, zai zama sakatare.

Gwamnan ya ce za a gudanar da binciken gawarwaki domin gano ainihin musabbabin mutuwar, yayin da DSS, Rundunar ’Yan Sanda da NSCDC su ma suka kafa kwamitocin bincike.

Gwamnatin ta ce Shugaban NSCDC na ƙasa ya dakatar da Kwamandan hukumar na Jihar Neja, Suberu Siyaka Aniviye, da tawagarsa domin ba da damar gudanar da bincike.

Gwamnatin ta kuma ayyana zaman makoki na kwanaki uku, tare da soke babban taron jamʼiyyar APC da aka shirya gudanarwa a Minna ranar Asabar.

Kazalika Gwamnatin ta rufe ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a yankin M.I. Wushishi.

Kungiyar kare haƙƙin bilʼadama ta Amnesty International ta nemi a yi ƙwaƙƙwaran bincike kan lamarin, yayin da lauyoyin nan A. A. Askira da Barr. Abba Hikima Fagge su ma suka nemi a gudanar da cikakken bincike da ɗaukar mataki kan duk wanda aka samu da alhakin abin da ya faru.

Har yanzu ba a tabbatar da ainihin musabbabin mutuwar mutane 37 ba a hukumance.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here