Managarciya

Gwamnatin Katsina ta tabbatar da rasuwar tsohon Janar na Soja a Hannun ‘yan bindiga

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da mutuwar tsohon mai magana da Yawun Rundunar sojin Najeriya Janar Rabe Abubakar Rasuwa A Hannun ’Yan Bindiga

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da rasuwar tsohon babban hafsan sojin Najeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya), wanda ya rasu yayin da yake tsare a hannun ’yan bindiga bayan sace shi.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Harkokin Tsaro da Cikin Gida na jihar, Dakta Nasiru Mu’azu, ya fitar, gwamnatin ta bayyana cewa duk da kokarin da ta yi tare da jami’an tsaro domin ganin an kubutar da marigayin cikin koshin lafiya, lamarin ya kare da wannan babban rashi.

Sanarwar ta ce marigayin ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka hada da ciwon sukari da hawan jini yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana rasuwar tsohon janar din a matsayin babban rashi ga iyalansa, Jihar Katsina da kuma Najeriya baki daya, yana mai cewa wannan wani lokaci ne na bakin ciki da ke nuna bukatar kara hada kai wajen yaki da matsalar ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki tare da gwamnatin tarayya da jami’an tsaro domin tabbatar da an hukunta wadanda ke da hannu a wannan mummunan lamari tare da kawo karshen matsalar rashin tsaro.

Exit mobile version