Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta kama wasu mutane biyar bisa zargin sanya T-shirts ɗauke da rubutun “Tinubu Must Go” a Maiduguri.
A cewar wata takardar ’yan sanda da Sahara Reporters ta wallafa, ana zargin mutanen da haɗa baki wajen buga T-shirts ɗin da nufin haddasa rikicin zaman lafiya a yankin West End Roundabout da ke Maiduguri.
’Yan sandan sun tuhume su da laifukan haɗa baki, tunzura jama’a, haddasa tashin hankali da kuma tayar da zaune tsaye.
Rahoton ya ce an gurfanar da mutanen gaban kotu, sannan aka tura su gidan yari yayin da shari’ar ke ci gaba.
