Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya amince da ƙirƙirar sabuwar Gundumar Shiko a Ƙaramar Hukumar Dandi, tare da naɗa sabbin shugabannin ƙauyuka huɗu a Ƙaramar Hukumar Argungu.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi da Harkokin Sarautun Gargajiya ta Jihar Kebbi, Alhaji Garba Umar Dutsinmari, ya sanya wa hannu, wadda aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Lahadi.
A cewar sanarwar, an ƙirƙiri sabuwar Gundumar Shiko ne daga cikin Gundumar Fana ta Ƙaramar Hukumar Dandi, inda aka naɗa Alhaji Garba Zarummai Fana a matsayin Shugaban Gundumar.
Sabuwar Gundumar Shiko ta ƙunshi ƙauyuka shida, waɗanda suka haɗa da Gudurege Shiko, Zarummai Shiko, Maiyaki Ona, Maiyamma R/Maikabi, Kokari Gorun Malam da Magaji Shiko.
Baya ga ƙirƙirar sabuwar gundumar, Gwamna Nasir Idris ya kuma amince da naɗa sabbin shugabannin ƙauyuka huɗu a Ƙaramar Hukumar Argungu.
Waɗanda aka naɗa sun haɗa da Muhammadu Dikko, wanda zai jagoranci Ƙauyen Gotomo da ke ƙarƙashin Gundumar Alwasa.
Sauran sun haɗa da Misbahu Sama’ila, wanda aka naɗa Shugaban Ƙauyen Dawakin Sarki ƙarƙashin Gundumar Yamman Argungu; Rabi’u Tsalhatu Galadima, sabon Shugaban Ƙauyen Gungu, shi ma ƙarƙashin Gundumar Yamman Argungu; da kuma Adamu Abubakar, wanda aka naɗa Shugaban Ƙauyen Magaji II ƙarƙashin Gundumar Gulma.
Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Sarautun Gargajiya, Alhaji Garba Umar Dutsinmari, ya bayyana cewa an gudanar da wannan tsari ne bisa tanadin Dokar Ƙananan Hukumomin Jihar Kebbi ta shekarar 2008.
Ya ce Sashe na 10, ƙananan sassa na (A) da (B) na dokar sun bai wa hukumomin da abin ya shafa damar ƙirƙirar gundumomi da kuma naɗa shugabannin gundumomi.
Kwamishinan ya kuma buƙaci sabbin masu riƙe da muƙaman gargajiyar da aka naɗa da su gudanar da ayyukansu cikin ladabi, gaskiya, riƙon amana da bayyana gaskiya, tare da jajircewa wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.
Ya ce naɗe-naɗen sun yi la’akari da kyawawan tarihin ayyukan waɗanda aka zaɓa da kuma gudunmawar da suka bayar a baya wajen ci gaban al’ummominsu.
Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana cewa ƙirƙirar sabuwar gundumar da kuma naɗa sabbin shugabannin ƙauyukan na daga cikin matakan ƙarfafa tsarin shugabanci na gargajiya da kusantar shugabanci ga al’umma.






